10 Milagres de Jesus na Bíblia: Lista com versículos e explicação
Os milagres de Jesus são muito mais do que demonstrações de poder sobrenatural; eles são sinais que confirmam sua divindade e missão. Ao longo dos Evangelhos, vemos Cristo curando enfermos, dominando a natureza e vencendo a morte.
Neste guia, selecionamos 10 milagres de Jesus na Bíblia, organizados com referências e uma breve explicação sobre o impacto espiritual de cada um deles.
Os principais milagres de Jesus nos Evangelhos
1. Transformação da Água em Vinho
Referência: João 2:1-11
Explicação: Ocorreu nas Bodas de Caná. Sendo o seu primeiro milagre público, Jesus demonstrou autoridade sobre a matéria e a natureza, revelando sua glória aos discípulos e abençoando a instituição da família.
Yesu ya mai da ruwa ya zama ruwan inabi
A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can, aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, "Ba su da sauran ruwan inabi."
Yesu ya ce, "Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna."
Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, "Ku yi duk abin da ya faɗa."
Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.
Sai Yesu ya ce wa bayin, "Ku ciccika tulunan da ruwa." Suka kuwa ciccika su fal.
Sa’an nan ya ce musu, "Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin."
Suka yi haka. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, "Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu."
Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.
2. Cura do cego de nascença
Referência: João 9:1-12
Explicação: Jesus usa lodo para curar um homem que nunca havia enxergado. Este milagre prova que Ele é a Luz do Mundo e tem poder para restaurar o que nasceu com defeito.
Yesu ya warkar da mutumin da aka haifa makaho
Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, "Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?"
Sai Yesu ya ce, "Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya."
Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. Ya ce masa, "Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam" (kalman nan tana nufin "Aikakke"). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, "Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?" Waɗansu suka ce shi mana.
Waɗansu kuwa suka ce, "A’a, ya dai yi kama da shi."
Amma shi ɗin ya ce, "Ƙwarai kuwa ni ne."
Sai suka ce, "To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?"
Ya amsa ya ce, "Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari."
Suka tambaye shi suka ce, "Ina mutumin yake?"
Ya ce, "Ban sani ba."
3. Multiplicação dos pães e peixes
Referência: Mateus 14:13-21
Explicação: Com apenas cinco pães e dois peixes, Jesus alimentou mais de 5 mil homens. Este sinal revela Cristo como o Pão da Vida, aquele que supre todas as nossas necessidades.
Yesu ya ciyar da dubu biyar
Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa. Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.
Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, "Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci."
Yesu ya amsa, "Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci."
Suka ce, "Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan."
Ya ce, "Ku kawo mini su a nan." Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.
4. Jesus acalma a tempestade
Referência: Marcos 4:35-41
Explicação: Com uma ordem, o vento e o mar se aquietam. O milagre ensina sobre a paz que excede o entendimento e a autoridade do Messias sobre a criação.
Yesu ya kwantar da iska
A wannan rana, da yamma, sai ya ce wa almajiransa, "Mu ƙetare zuwa wancan hayi." Da suka bar taron, sai suka tafi tare da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa. Akwai waɗansu jiragen ruwa kuma tare da shi. Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa. Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, "Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?"
Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, "Shiru! Ku natsu!" Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.
Sai ya ce wa almajiransa, "Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?"
Suka tsorata, suka ce wa juna, "Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!"
5. Cura da mulher com fluxo de sangue
Referência: Marcos 5:25-34
Explicação: Uma cura que aconteceu pelo toque da fé. Jesus mostra que está atento ao sofrimento individual e que a fé é o canal para receber o milagre.
A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, domin ta yi tunani cewa, "Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke." Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.
Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, "Wa ya taɓa rigata?"
Sai almajiransa suka ce, "Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ "
Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi. Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru. Sai ya ce mata, "Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki."
6. Libertação do endemoninhado Gadareno
Referência: Marcos 5:1-20
Explicação: Jesus liberta um homem dominado por uma legião de espíritos. É a prova clara de sua autoridade absoluta sobre o reino das trevas.
Warkar da mai aljanu
Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa. Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma. Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi. Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai.
Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya yi ihu da babbar murya ya ce, "Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!" Gama Yesu ya riga ya ce masa, "Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!"
Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, "Mene ne sunanka?"
Sai ya amsa ya ce, "Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa." Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin.
A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, "Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu." Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.
Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru. Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro. Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun. Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu.
Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi. Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, "Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai." Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
7. Ressurreição da filha de Jairo
Referência: Marcos 5:21-43
Explicação: Jesus demonstra que a morte para Ele é como o sono. Ele restaura a vida de uma criança, trazendo esperança para uma família desesperada.
Yarinya da ta mutu da mace marar lafiya
Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin. Sai ɗaya a cikin masu mulkin majami’a, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa, ya roƙe shi da gaske ya ce, "Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu." Sai Yesu ya tafi tare da shi.
Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe. A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, domin ta yi tunani cewa, "Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke." Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.
Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, "Wa ya taɓa rigata?"
Sai almajiransa suka ce, "Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ "
Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi. Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru. Sai ya ce mata, "Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki."
Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, "Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam."
Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, "Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai."
Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub. Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa. Sai ya shiga ciki, ya ce musu, "Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi." Sai suka yi masa dariya.
Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take. Sai ya kama hannunta ya ce mata, "Talita kum!" (Wato, "Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!"). Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai. Sai ya ba da umarni mai tsanani, kada kowa yă san kome game da wannan. Sai ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.
8. Jesus anda sobre as águas
Referência: Mateus 14:22-33
Explicação: Ao caminhar sobre o Mar da Galileia, Jesus mostra que não está sujeito às leis da física. O episódio também serve para tratar a fé e a dúvida no coração de Pedro.
Yesu ya yi tafiya a kan ruwa
Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron. Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai, jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi.
Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin. Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, "Fatalwa ce."
Amma nan da nan Yesu ya ce musu, "Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro."
Sai Bitrus ya amsa ya ce, "Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan."
Ya ce, "Zo."
Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu. Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, "Ubangiji, ka cece ni!"
Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, "Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?"
Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta. Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, "Gaskiya kai Ɗan Allah ne."
9. Cura do paralítico
Referência: Marcos 2:1-12
Explicação: Jesus cura o corpo, mas primeiro perdoa os pecados. Este milagre estabelece que sua missão principal é a reconciliação espiritual do homem com Deus.
Yesu ya warkar da shanyayye
Bayan ’yan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida. Mutane suka taru da yawa har ma babu wuri, ko a bakin ƙofa ma, sai ya yi musu wa’azin bishara. Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, "Saurayi, an gafarta zunubanka."
To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, "Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?"
Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, "Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai." Sai ya ce wa shanyayyen, "Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida." Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, "Ba mu taɓa ganin abu haka ba!"
10. Ressurreição de Lázaro
Referência: João 11:1-44
Explicação: O milagre mais impactante antes da crucificação. Ao ressuscitar alguém morto há quatro dias, Jesus declara: "Eu sou a ressurreição e a vida".
Mutuwar Lazarus
To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, "Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya."
Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, "Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan." Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus. Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
Sai ya ce wa almajiransa, "Mu koma Yahudiya."
Sai suka ce, "Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?"
Yesu ya amsa ya ce, "Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske."
Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, "Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi."
Almajiransa suka ce, "Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi." Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, "Lazarus ya mutu, amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa."
Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, "Mu ma mu je, mu mutu tare da shi."
Yesu ya yi wa ’yan’uwan Lazarus mata ta’aziyya
Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima, Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu. Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
Sai Marta ta ce wa Yesu, "Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba. Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa."
Yesu ya ce mata, "Ɗan’uwanki zai sāke tashi."
Marta ta amsa ta ce, "Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe."
Yesu ya ce mata, "Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu; kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?"
Sai ta ce masa, "I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya."
Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, "Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki." Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa. Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi. Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.
Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, "Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba."
Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. Sai ya yi tambaya ya ce, "Ina kuka sa shi?"
Suka amsa suka ce, "Ubangiji zo ka gani."
Yesu ya yi kuka.
Sai Yahudawa suka ce, "Dubi yadda yake ƙaunarsa!"
Amma waɗansunsu suka ce, "Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?"
Yesu ya tā da Lazarus daga matattu
Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse. Sai Yesu ya ce, "Ku kawar da dutsen."
Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, "Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can."
Sai Yesu ya ce, "Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?"
Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, "Uba, na gode maka da ka saurare ni. Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni."
Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, "Lazarus, ka fito!" Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi.
Yesu ya ce musu, "Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi."
Conclusão
Os milagres de Jesus revelam sua autoridade sobre a natureza, as enfermidades, o mundo espiritual e até a morte. Eles não são apenas demonstrações de poder, mas sinais que apontam para sua identidade e missão.
Ao estudar esses milagres, é possível compreender melhor o papel de Jesus e a mensagem central do Evangelho.
Se este conteúdo ajudou você a entender os milagres de Jesus na Bíblia, compartilhe este artigo para que mais pessoas também conheçam esses ensinamentos.