10 versículos para fortalecer os laços familiares
A Bíblia enfatiza a importância da família e nos ensina como viver em harmonia com nossos entes queridos. Neste artigo, vamos explorar 10 versículos bíblicos que podem fortalecer os laços familiares e nos ajudar a refletir sobre o papel da família à luz da Palavra de Deus.
Versículos
1. Provérbios 22:6
Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
2. Salmos 127:3
’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,
yara lada ne daga gare shi.
3. Colossenses 3:20
’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.
4. Êxodo 20:12
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
5. Provérbios 1:8
Jan kunne game da jaraba
Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
6. Josué 24:15
Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."
7. Deuteronômio 6:6-7
Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
8. Salmo 128:3
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya
a cikin gidanka;
’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun
kewaye da teburinka.
9. Provérbios 15:20
Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa,
amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.
10. Efésios 5:25
Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.
Esses versículos sobre a família nos lembram da importância de honrar, amar e cuidar uns dos outros. Medite neles e viva em harmonia, de acordo com os ensinamentos de Deus.
Compartilhe este artigo para inspirar outras famílias a serem fortalecidas pela Palavra de Deus.
Deus abençoe!