A fé vem pelo ouvir
A fé vem pelo ouvir, e o ouvir pela Palavra de Cristo. Quando a Palavra é proclamada, a fé nasce nos corações. Ouvir a Deus é o primeiro passo para crer e seguir.
A fé vem pelo ouvir
A fé vem pelo ouvir, e o ouvir pela Palavra de Cristo. Quem ouve a Palavra crê e obtém a salvação eterna.
Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, gama, "Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto."
To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, "Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!"
Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, "Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?" Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.
Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji?
An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.
"Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.
Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.
Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina. Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban. Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.
Ouvir e obedecer
Felizes os que ouvem a Palavra de Deus e a praticam. Quem tem ouvidos ouça o que o Espírito diz.
Yesu ya amsa ya ce, "A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita."
Duk mai kunnen ji, bari yă ji."
Ya ce, musu, "Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.
A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,
" ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba;
za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.
Gama zuciyar mutanen nan ta taurare;
da ƙyar suke ji da kunnuwansu,
sun kuma rufe idanunsu.
Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu,
su kuma ji da kunnuwansu,
su gane a zuciyarsu,
su kuwa juya, in kuma warkar da su.’
Amma idanunku masu albarka ne domin suna gani, haka ma kunnuwanku domin suna ji.
Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, "Ku saurara ku kuma gane.
Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni;
ku saurare ni, don ranku ya rayu.
Zan yi madawwamin alkawari da ku,
zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.
Ya ce, "Je ka ka faɗa wa wannan mutane,
" ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba;
Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’
Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;
kunnuwansu su kurunce,
idanunsu kuma su makance.
In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,
su ji da kunnuwansu,
su fahimta da zuciyarsu,
su kuma juyo a kuma warkar da su."
Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi.