Pular para o conteúdo
Publicidade

A última palavra vem do Senhor

Por Bíblia Online

A última palavra pertence ao Senhor. Os planos do homem estão sujeitos à soberania de Deus. Ele rege toda a história e nenhum de seus propósitos pode ser frustrado.

Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke,

amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.

Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa,

har ma da mugaye domin ranar masifa.

Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,

shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.

Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?

Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?

Ubangiji ya ce wa Musa, "Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu."

haka maganata da take fitowa daga bakina.

Ba za koma gare ni wofi ba,

amma za cika abin da nake so

ta kuma cika abin da na aike ta yi.

"Ni ne Ubangiji Allah na dukan yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni?

"Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa;

ba wanda zai iya ɓata shirinka.

Ubangiji yana yin abin da ya ga dama,

a sammai da kuma a duniya,

cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.

Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.

Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za taɓa shuɗe ba.

Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ranar da na yi magana ke nan.

Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan ɓace. A maimakon haka, ya kamata ku ce, "In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan."

Seja o primeiro