Admiração
O temor do Senhor é o princípio da sabedoria. A admiração reverente por Deus é a postura que produz conhecimento, obediência e bênção na vida do crente.
Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye sun rena hikima da horo.
"Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,
kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji
da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.
Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;
ina ƙin girman kai da fariya,
halin mugunta da kuma muguwar magana.
Sauƙinkai da tsoron Ubangiji
sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
Wannan zai ba wa jikinka lafiya
yă kuma adana ƙasusuwanka.
Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
Yanzu an ji kome;
ga ƙarshen magana.
Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa,
gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.
Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.
Gare shi ne madawwamin yabo.
Yabi Ubangiji.
Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.
Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
Allah yă sa mana albarka,
dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.
Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.
Ku ji tsoron Ubangiji
Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?
Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.
Saboda ungozomomin suna tsoron Allah, sai Allah ya ba su iyalan kansu.
Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.
Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.
"Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki
ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.