Pular para o conteúdo
Publicidade

Adoração

Por Bíblia Online

A adoração é a resposta do coração humano à majestade de Deus. Deus é Espírito e importa que os que o adoram o adorem em espírito e em verdade — com todo o ser.

Adorar em espírito

Deus é Espírito e importa que os adoradores o adorem em espírito e em verdade. A adoração verdadeira brota do coração.

Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma."

Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma."

Sai Yesu ya ce, "Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.

Sai mutumin ya ce, "Ubangiji, na gaskata," ya kuma yi masa sujada.

Sai Yesu ya ce masa, "Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa."

Yesu ya amsa ya ce, "A rubuce yake, Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa."

Hadayu masu rai

Saboda haka, ina roƙonku, yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.

Hadayu masu rai

Saboda haka, ina roƙonku, yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.

Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.

A rubuce yake cewa,

" Muddin ina raye,in ji Ubangiji,

kowace gwiwa za durƙusa a gabana;

kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ "

Louvor e reverência

Vinde, adoremos e prostremo-nos. Louvai ao Senhor! Todo ser que respira louve o nome glorioso do Senhor.

Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

Yabi Ubangiji.

Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;

yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;

yabe shi saboda mafificin girmansa.

Yabe shi da ƙarar kakaki,

yabe shi da garaya da molo,

yabe shi da ganga kuna taka rawa,

yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

yabe shi da kuge mai ƙara,

yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

Bari kowane abu mai numfashi yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji.

Bari kowane abu mai numfashi yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji.

Ku shiga ƙofofinsa da godiya

filayen gidansa kuma da yabo;

ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;

ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

Ku rera ɗaukaka ga sunansa;

ku sa yabonsa zama da ɗaukaka!

Ku ce wa Allah, "Ayyukanka da banmamaki suke!

Ikonka da girma yake

har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

Dukan duniya sun rusuna a gabanka

suna rera yabo gare ka,

suna rera yabo ga sunanka." Sela

Na yi kuka gare shi da bakina;

yabonsa yana a harshena.

Dukan al’umman da ka yi

za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji;

za su kawo ɗaukaka ga sunanka.

Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki;

kai kaɗai ne Allah.

Yabi Ubangiji, ya raina;

dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

Ya Allah, kai ne Allahna,

da nacewa na neme ka;

raina yana ƙishinka,

jikina yana marmarinka,

cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye

inda babu ruwa.

Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,

leɓunana za su ɗaukaka ka.

Zan yabe ka muddin raina,

kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.

Declarações de adoração

Tu és digno, Senhor, de receber glória e honra! Ao Senhor pertence a grandeza, o poder, a glória e a majestade.

"Ya Ubangijinmu da Allahnmu,

ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,

domin ka halicci dukan abubuwa,

kuma ta wurin nufinka aka halicce su

suka kuma kasance."

Ya ce da babbar murya, "Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada."

Wane ne ba zai ji tsoronka,

kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?

Gama kai kaɗai ne mai tsarki.

Dukan al’ummai za su zo

su yi sujada a gabanka,

gama an bayyana ayyukan adalcinka."

Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada. Amma ya ce mini, "Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!"

Girma da iko

da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,

gama kome a sama da ƙasa naka ne.

Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;

an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.

Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

ƙaunarsa madawwamiya ce.

Ku yi kuka, ku ce, "Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;

tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,

don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,

don mu ɗaukaka a cikin yabonka."

Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,

daga madawwami zuwa madawwami.

Sai dukan mutane suka ce, "Amin." Suka kuma "Yabi Ubangiji."

Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

ƙaunarsa madawwamiya ce.

Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;

ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.

Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri

ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

don a sunan Yesu kowace gwiwa za durƙusa,

a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

kowane harshe kuma furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,

don ɗaukakar Allah Uba.

Sacrifício de louvor

Por meio de Jesus ofereçamos sempre sacrifício de louvor. Cantai ao Senhor, celebrai em salmos — enchei-vos do Espírito.

Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.

Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro, gama "Allahnmu wuta ne mai cinyewa."

Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.

Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.

Allah na dukan ta’aziyya

Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.

Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi.

Adoração como vida

Exaltai ao Senhor, prostrai-vos ante o escabelo dos seus pés. A adoração genuína transforma o adorador e agrada o Criador.

Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu

ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa;

shi mai tsarki ne.

Bakina ya cika da yabonka,

ina furta darajarka dukan yini.

Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,

ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;

sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.

Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,

shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.

Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa

zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.

Zan furta sunanka ga yan’uwana;

cikin taron masu sujada zan yabe ka.

Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi!

Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi!

Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!

Na buɗe hannuwana gare ka;

raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela

Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da kuma Allahna.

Na ce wa Ubangiji, "Kai ne shugabana;

in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau."

Ku bauta wa Ubangiji da tsoro

ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.

Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;

zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.

Falsa adoração

Não terás outros deuses diante de mim. Não adorarás ídolos. A adoração exclusiva ao Senhor é mandamento inegociável.

Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,

Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi.

Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije sauko, tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa. Lokacin da mutane suka ga al’amudin girgije a tsaye a ƙofar tentin, sai duk su miƙe tsaye su yi sujada, kowa a ƙofar tentinsa.

"Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,

ya zama cetona.

Shi Allahna ne, zan yabe shi.

Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.

Wane ne cikin alloli,

ya yi kamar ka, ya Ubangiji?

Wane ne kamar ka,

mai ɗaukaka cikin tsarki,

mai banrazana cikin ɗaukaka,

mai aikata al’ajabai?

Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku.

Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.

A can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku da iyalanku za su ci, su kuma yi farin ciki a kome da kuka sa hannunku a kai, domin Ubangiji Allahnku zai albarkace ku.

Suka sa shi kishi saboda baƙin allolinsu,

suka husata shi da gumakan banƙyamarsu.

Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba,

ga allolin da ba su sani ba,

ga allolin da aka shigo da su daga baya,

allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba.

Kuka rabu da Dutsen da ya zama mahaifi gare ku;

kuka manta da Allahn da ya haife ku.

Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada,

Ubangiji ya ce,

"Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu

suka kuma girmama ni da leɓunansu,

amma zukatansu suna nesa daga gare ni.

Sujadar da suke mini

cike take da dokokin da mutane suka koyar.

Yabo ga Ubangiji

Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,

gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,

abubuwan da aka shirya tun da.

Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa,

" Kun kawo mini hadayu da sadakoki

shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?

Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek,

da tauraron allahnku Refan,

gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.

Saboda haka zan aike ku zuwa bauta gaba da Babilon.

Kada ku yarda wani ɓata ku, cewa shi wani abu ne don ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka. Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yi girma.

Kada ku bar wani ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. Zai yi gāba kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.

Exemplos de adoração

Jó adorou em meio ao sofrimento. Esdras adorou na restauração. Paulo e Silas adoraram na prisão — e Deus respondeu.

Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada ya ce,

"Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,

tsirara kuma zan koma.

Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;

yabo ya tabbata ga Ubangiji."

Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa,

"Shi nagari ne;

ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce."

Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.

Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su.

"Kai mai girma ne, ya Ubangiji Mai Iko Duka! Babu wani kamar ka, babu kuma wani Allah sai kai; kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

"Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji

babu wani, in ban da kai;

babu wani dutse kamar Allahnmu.

Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, "Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin."

"Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo.

Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba,

ba kuma ya’ya a kuringar inabi,

ko da yake zaitun bai ba da amfani ba,

gonaki kuma ba su ba da abinci ba,

ko da yake babu tumaki a garke,

ba kuma shanu a turaku,

duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,

zan yi murna da Allah Mai Cetona.

Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.

Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

Seja o primeiro