O adultério
O adultério é pecado grave que destrói alianças, famílias e vidas. A Bíblia condena firmemente a infidelidade conjugal e chama à pureza, fidelidade e santidade no casamento.
A lei de Deus
Não adulterarás. Quem comete adultério destrói a própria alma. A Palavra de Deus é clara e direta sobre este pecado.
Ba za ka yi zina ba.
" ‘In mutum ya yi zina da matar wani, da matar maƙwabcinsa, dole a kashe su biyu da suka yi zinan.
" ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.
Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;
duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.
Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;
duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.
Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,
kuma kunyarsa za tă dawwama.
Gama kishi kan tā da hasalar miji,
kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.
Ba zai karɓi duk wata biya ba;
zai ƙi cin hanci, kome yawansu.
Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa
ba tare da rigunansa sun ƙone ba?
Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi
ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?
Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;
babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.
Jesus ensina
Quem olhar para uma mulher com intenção impura já adulterou no coração. Jesus elevou o padrão da pureza.
"Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.
Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.
Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.
Ya amsa ya ce, "Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan."
"Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi.
suka kuma ce wa Yesu, "Malam, an kama wannan mace tana zina. A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?" Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi.
Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, "In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse." Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.
Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, "Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?"
Ta ce, "Ba kowa, ranka yă daɗe."
Sai Yesu ya ce, "Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi."
Armadilhas e consequências
Os lábios da mulher estranha destilam mel, mas o seu fim é amargo. Fuja da imoralidade — o adultério escraviza.
Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma,
maganarta tana da sulɓi fiye da mai;
amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya,
mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.
Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa;
sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.
Ba ta wani tunanin rayuwa;
hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.
Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma,
maganarta tana da sulɓi fiye da mai;
amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya,
mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.
Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa;
sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.
Ba ta wani tunanin rayuwa;
hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.
Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
kada ku juye daga abin da nake faɗa.
Ku yi nesa da hanyarta,
kana ku je kusa da ƙofar gidanta,
don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu
da kuma shekarunku ga wani marar imani,
Ku yi nesa da hanyarta,
kana ku je kusa da ƙofar gidanta,
don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu
da kuma shekarunku ga wani marar imani,
don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku
wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.
A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi,
sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.
Za ku ce, "Me ya sa na ƙi horo!
Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!
Ban yi biyayya da malamaina ba
ko in saurari masu koyar da ni.
Na zo gab da hallaka gaba ɗaya
a tsakiyar dukan taron."
Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,
bari mamanta su ishe ka kullum,
bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali?
Don me za ka rungume matar wani?
Gama gidanta yana kai ga mutuwa
hanyarta kuma ga ruhohin matattu.
Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa
ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.
Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi;
duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.
Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.
Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.
Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.
Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;
Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.
Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya. Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta.