Publicidade

Agradecimento a Deus

Por Bíblia Online

Agradecer a Deus é louvor, adoração e reconhecimento da sua soberania. Dai graças ao Senhor porque Ele é bom — a sua misericórdia dura para sempre!

Bari mu zo gabansa da godiya

mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

Ku shiga ƙofofinsa da godiya

filayen gidansa kuma da yabo;

ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

Yabi Ubangiji.

Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;

ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya;

kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.

Rera wa Ubangiji waƙar godiya;

ku kada garaya ga Allahnmu.

Zan yabe sunan Allah cikin waƙa

in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.

Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;

zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.

Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki

zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka,

muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.

Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.

Godiya da addu’a

Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.

Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

Godiya saboda bangaskiyar Tessalonikawa

Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’oinmu. Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.

Godiya

Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu.

Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina.

To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, riɓanya shi, kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za zama sanadin godiya ga Allah.

Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

Mata da maza

Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.

Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. Kowa ya ci, ya ƙoshi, almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-