Pular para o conteúdo
Publicidade

Agradecimento pela vida

Por Bíblia Online

Agradecer pela vida é reconhecer que cada respiração é dom de Deus. Toda criatura que tem fôlego louve ao Senhor — porque Ele nos formou e nos sustenta com amor.

Bari kowane abu mai numfashi yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji, ya raina.

Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina;

zan rera yabo ga Allahna muddin raina.

Gama ka halicci ciki-cikina;

ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

sa’ad da aka yi ni asirce.

Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

Idanunka sun ga jikina marar fasali;

dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

kafin ɗayansu kasance.

Zan rera ga Ubangiji dukan raina;

zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.

Bari tunanina gamshe shi,

yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.

Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.

Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;

mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

Ku shiga ƙofofinsa da godiya

filayen gidansa kuma da yabo;

ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa!

Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

Suna biki a yalwar gidanka;

kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.

Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai

cikin haskenka mukan ga haske.

Zan girmama ka Ya Ubangiji,

gama ka tsamo ni daga zurfafa

ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.

Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako

ka kuwa warkar da ni.

Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;

ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.

Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;

zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.

Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;

zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.

Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

Albarkun ruhaniya a cikin Kiristi

Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.

Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!

kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

Fifikon Kiristi

Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.

Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda ƙasa mai kyau da ya ba ku.

Ya Ubangiji, ka goyi bayana;

ka fanshi raina.

Na nutsa har ƙarƙashin tuddai;

a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada.

Amma ka dawo da raina daga rami,

Ya Ubangiji Allahna.

"Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni,

na tuna da kai ya Ubangiji,

addu’ata kuma ta kai gare ka,

a haikalinka mai tsarki.

Seja o primeiro