Agradecimento
O agradecimento é a linguagem natural do cristão. Em tudo dai graças! A gratidão a Deus transforma a perspectiva, fortalece a fé e produz alegria em todos os tempos.
Dar graças sempre
Em tudo dai graças, porque esta é a vontade de Deus em Cristo Jesus para convosco. A gratidão é atitude fundamental.
ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.
Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.
Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.
Louvor e gratidão
Entrai pelas portas com ação de graças. Rendei graças ao Senhor porque Ele é bom e a sua bondade dura para sempre.
Ku shiga ƙofofinsa da godiya
filayen gidansa kuma da yabo;
ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
Yana da kyau a yabi Ubangiji
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
don a yi shelar ƙaunarka da safe
amincinka kuma da dare,
Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni,
ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah."
Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya;
kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka,
muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
Expressões de gratidão
Graças a Deus pelo seu dom inefável! A gratidão se expressa em oração, louvor e generosidade para com os outros.
Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!
Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu.
Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya.
Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.
Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.
Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
" ‘ "Ubangiji yă albarkace ku,
yă kuma kiyaye ku;
Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku,
yă kuma yi muku alheri;
Ubangiji yă dube ku da idon rahama,
yă kuma ba ku salama." ’
Amma ni, da waƙar godiya,
zan miƙa tawa hadaya gare ka.
Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi.
Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji."
Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa.
Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina.
ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina.
Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro,
Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka.
Da ya gan su sai ya ce, "Ku je ku nuna kanku ga firistoci." Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.
Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
Yesu ya yi tambaya ya ce, "Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?" Sai ya ce masa, "Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai."
Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, suka yi kira da babbar murya, suka ce, "Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!"
Da ya gan su sai ya ce, "Ku je ku nuna kanku ga firistoci." Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.
Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
Yesu ya yi tambaya ya ce, "Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?" Sai ya ce masa, "Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai."
Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.