Publicidade

Ajuda ao próximo

Por Bíblia Online

Ajudar o próximo é mandamento de Deus e expressão prática da fé. A Bíblia ensina que a fé sem obras é morta — e que servir ao menor dos irmãos é servir a Cristo.

Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni, da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.

"Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?

"Sarkin zai amsa ya ce, Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.

Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.

Haka ma, bari haskenku haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku."

Sai taron suka tambaye shi, suka ce "Me za mu yi ke nan?"

Ya amsa ya ce, "Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yi haka."

Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba. Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.

Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.

Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, Bayarwa ta fi karɓa albarka."

Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a. Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba. Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.

Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.

Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba.

Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.

Duk wanda yake sata, sai daina sata, dole kuma yi aiki, yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don sami abin da zai iya raba da masu bukata.

Bai kamata kowannenku kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai kula da sha’anin waɗansu ma.

Bangaskiya da ayyuka

Wanda amfani ne, yan’uwana, a ce wani ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za iya cetonsa kuwa? A ce wani ɗan’uwa ko yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, sai waninku ce masa, "Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura," amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.

In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?

Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne,

zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.

Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-