Ajuda
Deus é nosso auxílio e socorro em todo tempo. Ele não dorme nem cochila. O Senhor é nosso ajudador — não precisamos temer o que o homem possa nos fazer.
Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
Tabbatacce Allah ne mai taimakona,
Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.
Ceton adalai kan zo daga Ubangiji;
shi ne mafaka a lokacin wahala.
Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su;
yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su,
domin sukan nemi mafaka daga gare shi.
Zo da sauri ka taimake ni,
Ya Ubangiji Mai Cetona.
Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,
saboda ɗaukakar sunanka;
ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu
saboda sunanka.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya ji kukata na neman jinƙai.
Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba,
da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.
Gama ni ne Ubangiji Allahnka,
wanda ya riƙe ka da hannun damana
ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;
zan taimake ka.
Ka ba ni garkuwar nasararka;
ka sauko don ka sa in sami girma.
"Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.
Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,
Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.
Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.