Publicidade

Aliança

Por Bíblia Online

A aliança é o modo como Deus se relaciona com seu povo. Da aliança com Noé à Nova Aliança em Cristo, Deus se compromete com amor e fidelidade irrevogáveis.

Alianças com Israel

Deus firmou aliança com Abraão, Moisés e Davi. No arco-íris, na lei, nas promessas — Ele é o Deus da aliança.

Sai Allah ya ce wa Nuhu da ya’yansa, "Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku, da kowace halitta mai rai wadda ta kasance tare da kai; wato, tsuntsaye da dabbobin gida da kuma dukan namun jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin; wato, kowane mai rai na duniya. Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba."

Allah ya kuma ce, "Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa. Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya.

Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba."

Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya.

A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, "Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan, ƙasar Keniyawa, Kenizziyawa, Kadmoniyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Refahiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa."

Abram ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, Allah kuma ya ce masa, "Gare ni kam, wannan shi ne alkawarina da kai, za ka zama mahaifin al’ummai masu yawa. Ba za a ƙara kiranka Abram ba; sunanka zai zama Ibrahim, gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa. Zan sa ka azurta sosai, zan yi al’ummai daga cikinka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka, zan kafa alkawarina kamar madawwamin alkawari tsakanina da kai da kuma zuriyarka bayanka har tsararraki masu zuwa, in zama Allahnka da kuma Allahn zuriyarka a bayanka. Dukan ƙasar Kan’ana inda kake baƙo a yanzu, zan ba da ita a matsayin madawwamiyar mallaka gare ka da kuma zuriyarka a bayanka, zan kuma zama Allahnsu."

Sa’an nan Allah ya ce wa Ibrahim. "Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, kai da zuriyarka bayanka, har tsararraki masu zuwa. Wannan shi ne alkawarina da kai da kuma zuriyarka a bayanka, alkawarin da za ka kiyaye ke nan. Kowane namiji a cikinku kuwa za a yi masa kaciya. Za ku yi kaciya, za kuma zama alamar alkawari tsakanina da kai.

A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim,

Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce,

"Zan kafa iyakokinku daga Jan Teku zuwa Bahar Rum, daga hamada kuma zuwa Kogi. Zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kuwa kore su daga gabanku. Kada ku ƙulla yarjejjeniya da su, ko da allolinsu.

Sai Ubangiji ya ce, "Ga shi na yi alkawari da kai. A gaban dukan mutanenka zan yi abubuwan banmamakin da ba a taɓa yinsa a cikin wata al’umma a duniya ba. Mutanen da kuke zaune cikinsu za su ga aikin bantsoro, da Ni Ubangiji zan yi muku.

Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.

Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.

Ya furta alkawarinsa gare ku, Dokoki Goma, waɗanda ya umarce ku ku bi, ya kuma rubuta su a alluna biyu.

Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa.

Alianças renovadas

O povo renovava a aliança diante do Senhor. A fidelidade de Deus permanece mesmo quando o povo falha.

Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba. Da kaka Urdun yakan cika makil da ruwa. Duk da haka da zarar firistoci masu ɗauke da akwatin alkawari suka tsoma ƙafafunsu a gefen ruwa, sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko. Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.

Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari tsakanin Ubangiji da sarki da kuma mutane cewa za su zama mutanen Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane.

Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.

To, a lokacin, Sarki Yoram ya tashi daga Samariya, ya tattara sojoji daga dukan Isra’ila. Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, "Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?"

Sai sarkin Yahuda ya ce, "I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne."

Saboda haka Yonatan ya yi yarjejjeniya da gidan Dawuda cewa Ubangiji kawo dukan maƙiyin Dawuda ga mutuwa. Yonatan kuwa ya sa Dawuda ya sāke tabbatar masa rantsuwansa game da abokantakarsa da shi, gama yana ƙaunar Dawuda kamar ransa.

Ubangiji ya ce wa Musa, "Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba. Saboda haka ka faɗa masa cewa zan yi alkawarin salama da shi. Shi da zuriyarsa za su kasance da alkawari na zama firist har abada, saboda kishinsa domin ɗaukakar Allahnsa, ya kuma yi kafara domin Isra’ilawa."

Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.

Tohuwar sandar Haruna

Ubangiji ya ce wa Musa, "Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa. A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu. Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai. Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi."

Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu. Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.

Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ya’yan almon. Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.

Ubangiji ya ce wa Musa, "Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu." Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.

Ehud

Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda sun aikata wannan mugunta sai Ubangiji ya ba wa Eglon sarkin Mowab ƙarfi a kan Isra’ila. Da ya sami Ammonawa da Amalekawa suka haɗa hannu tare, sai Eglon ya tafi ya auka wa Isra’ila, suka ƙwace Birnin Dabino.

Nova Aliança

Eis que dias vêm em que farei nova aliança. Jesus é mediador de uma aliança superior, fundamentada em melhores promessas.

"Lokaci yana zuwa," in ji Ubangiji,

"sa’ad da zan yi sabon alkawari

da gidan Isra’ila

da kuma gidan Yahuda.

Ba zai zama kamar alkawarin

da na yi da kakanni kakanninsu ba

sa’ad da na kama su da hannu

na bishe su daga Masar,

domin sun take alkawarina,

ko da yake na zama miji a gare su,"

in ji Ubangiji.

"Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila

bayan wannan lokaci," in ji Ubangiji.

"Zan sa dokata a tunaninsu

in kuma rubuta ta a zukatansu.

Zan zama Allahnsu,

za su kuma zama mutanena.

Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,

ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, Ka san Ubangiji,

domin duk za su san ni,

daga ƙaraminsu har zuwa babba,"

in ji Ubangiji.

"Gama zan gafarta muguntarsu

ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba."

"Ga abin da Ubangiji yana cewa, In ka da alkawarina na rana da kuma alkawarina na dare, har dare da rana ba za su ƙara bayyana a ƙayyadaddun lokutansu ba, to, sai a da alkawarina da Dawuda bawana da alkawarina da Lawiyawan da suke firistoci masu hidima a gabana, Dawuda kuma ba zai ƙara kasance da zuriyar da za yi mulki.

Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.

Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.

Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.

Albarka da kuma gaisuwa ta ƙarshe

Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.

Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan. Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ya’yanta. Amma Urushalimar da take sama yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu.

Fidelidade da aliança

A aliança de Deus é eterna. Ele não quebra seu pacto nem altera o que saiu dos seus lábios.

Amma daga madawwami zuwa madawwami

ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,

adalcinsa kuma tare da ya’yansu,

tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa

suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

"Game da ni dai, ga alkawarina da su," in ji Ubangiji. "Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada," in ji Ubangiji.

" Zan yi alkawarin salama da su in kuma kawar wa ƙasar da namun jeji domin su zauna a hamada su kuma kwana a kurmi lafiya lau.

Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai."

Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai. A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama."

"Sai sarki Kudu zai yi ƙarfi ƙwarai, amma ɗaya daga cikin komandodinsa zai yi ƙarfi fiye da shi, zai kuma yi mulki masarautarsa da iko mai girma. Bayan yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta da kuma wanda ya goyi bayanta.

Wanda ya kai harin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai kafa kansa a Kyakkyawar Ƙasa zai kuma sami ikon da zai hallaka ta. Zai yunƙura zo da ƙarfin dukan masarautarsa zai kuma nemi haɗinkan sarkin Kudu. Zai kuma ba shi diyarsa aura don lalatar da mulkin, amma shirinsa ba zai yi nasara ba ko taimake shi ba.

"Na yi alkawari da idanuna

kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.

Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya,

daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,

wadda ta bar mijin ƙuruciyarta

ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-