Publicidade

Alma

Por Bíblia Online

A alma é a parte mais íntima do ser humano — sede da vida, dos afetos e do encontro com Deus. A Bíblia convida a cuidar da alma com zelo e a aquietá-la diante do Senhor.

A alma diante de Deus

Bendize ao Senhor, ó minha alma! A alma suspira por Deus como a corça suspira pelas águas — com sede de eternidade.

Yabi Ubangiji, ya raina;

dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

Ya Allah, kai ne Allahna,

da nacewa na neme ka;

raina yana ƙishinka,

jikina yana marmarinka,

cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye

inda babu ruwa.

Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da kuma Allahna.

Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai;

cetona na zuwa daga gare shi.

Zan jira Ubangiji, raina zai jira,

kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

Leɓunana za su yi sowa don farin ciki

sa’ad da na rera yabo gare ka,

ni, wanda ka fansa.

Dokar Ubangiji cikakkiya ce,

takan wartsakar da rai.

Farillan Ubangiji abin dogara ne,

suna mai da hikima da sauƙi.

Gama ka halicci ciki-cikina;

ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

Ka cece ni, ya Ubangiji,

daga leɓuna masu ƙarya

da kuma daga harsuna masu yaudara.

Cuidar da alma

Que aproveita ao homem ganhar o mundo inteiro e perder a sua alma? Buscar a Deus de toda alma é o caminho da vida.

Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?

Yesu ya amsa ya ce, " Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.

Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.

Amma daga can in kuka nemi Ubangiji Allahnku, da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, za ku same shi.

Amma ku yi hankali, ku kiyaye umarnai da kuma dokokin da Musa bawan Ubangiji ya ba ku. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya kan hanyarsa, ku yi biyayya da umarnansa, ku riƙe shi sosai, ku bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku."

"Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.

Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.

Ga abin da Ubangiji yana cewa,

"Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba;

ku nemi hanyoyin ,

ku tambaya inda hanyar mai kyau take, ku yi tafiya a kanta,

za ku kuwa sami hutu wa rayukanku.

Amma kun ce, Ba za mu bi ta ba.

Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,

mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.

Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-