Pular para o conteúdo
Publicidade

Amor fraternal

Por Bíblia Online

O amor fraternal é marca dos discípulos de Cristo. Nisto conhecerão que sois meus discípulos: se tiverdes amor uns aos outros.

Amar uns aos outros

Este é o meu mandamento: que vos ameis uns aos outros como Eu vos amei. O amor fraternal é testemunho ao mundo.

"Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna."

Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.

Ku ƙaunaci juna

Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna.

Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu.

Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin yan’uwanmu. In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.

Ƙaunar Allah da kuma tamu

Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah.

Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu. Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

Duk wanda ya ce, "Ina ƙaunar Allah," amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba. Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole ƙaunaci ɗan’uwansa.

Expressões de amor fraternal

Amai-vos com afeição fraternal. O amor cobre multidão de pecados. Perseverai no amor fraterno.

Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta yan’uwa. Kowa yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.

Ku yi ƙauna, gama ranar ta yi kusa

Kada hakkin kowa zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

Shan wahala saboda yin ayyuka alheri

A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.

Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

Yanzu kuwa game da ƙaunar yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna.

Gargaɗin ƙarshe

Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar yan’uwa. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba. Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.

Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

Yesu ya amsa ya ce, " Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka. Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. Ta biye kuma kamar ta farkon take. Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.

In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, "Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka," kun yi daidai.

Seja o primeiro