Aniversário de idoso
O aniversário de um idoso é celebração de uma vida longa e cheia de experiências com Deus. A Bíblia honra os cabelos brancos como coroa de glória e prova da fidelidade divina.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;
ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
Zan gode wa Ubangiji kullayaumi;
yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.
Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
Ka cika zuciyata da farin ciki
sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.
Ka sanar da ni hanyar rai;
za ka cika ni da farin ciki a gabanka,
da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
Abu guda na roƙi Ubangiji,
wannan shi ne na nema,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
dukan kwanakin raina,
in dubi kyan Ubangiji
in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,
don mu sami zuciyar hikima.
Furfura rawani ne mai daraja;
akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu,
furfura ita ce darajar tsofaffi.
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
"Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar! Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā.
" ‘ "Ubangiji yă albarkace ku,
yă kuma kiyaye ku;
Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku,
yă kuma yi muku alheri;
Ubangiji yă dube ku da idon rahama,
yă kuma ba ku salama." ’
Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.