Publicidade

Arca de noé

Por Bíblia Online

A arca de Noé é história de salvação e fidelidade. Deus instruiu Noé a construir a arca para salvar sua família e os animais do dilúvio — exemplo supremo de obediência e fé.

Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, "Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya. Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires, ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje. Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45. Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.

Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. "Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani.

Nuhu da matarsa da ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya. Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu. Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.

Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.

Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya. Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa.

Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.

Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu. A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat.

Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya. Sai ya saki kurciya don ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa. Amma kurciyar ba sami inda za sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi. Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba komo wurinsa ba.

A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe.

Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, "Fito daga jirgin, kai da matarka da ya’yanka maza da matansu. Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya."

Sai Allah ya ce wa Nuhu da ya’yansa, "Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku, da kowace halitta mai rai wadda ta kasance tare da kai; wato, tsuntsaye da dabbobin gida da kuma dukan namun jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin; wato, kowane mai rai na duniya. Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba."

Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya.

Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.

waɗanda ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa, ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.

Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-