Pular para o conteúdo
Publicidade

Autocontrole

Por Bíblia Online

O autocontrole é fruto do Espírito e virtude indispensável. A graça de Deus nos ensina a renunciar à impiedade e a viver com sobriedade, domínio próprio e piedade no mundo presente.

Fruto e virtude

O domínio próprio é fruto do Espírito. Acrescentai ao conhecimento o autocontrole. A disciplina interior produz maturidade.

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga yan’uwa; ga nuna alheri ga yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna.

Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. Yana koya mana mu ce, "A’a" ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-shaawacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani,

Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

Duk yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama.

Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

Dominar a si mesmo

Melhor é quem domina o seu espírito do que quem toma uma cidade. A cidade sem muros é quem não tem autocontrole.

Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi,

ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

Kamar birni da katangarsa sun rushe

haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa.

Wawa yakan nuna fushinsa a fili,

amma mai hikima kan kanne fushinsa.

Kada ka kauce dama ko hagu;

ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.

Wawa kan nuna fushinsa nan take,

amma mai la’akari kan ƙyale zargi.

Harshe yana da ikon rai da mutuwa,

kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.

Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

Saurarawa da kuma aikatawa

Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,

Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.

Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.

"Na yi alkawari da idanuna

kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.

Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada.

Seja o primeiro