Beleza
A verdadeira beleza vem de dentro. A Bíblia ensina que o encanto é enganoso e a formosura é vã, mas a mulher que teme ao Senhor — essa sim merece louvor.
Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, "Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya."
Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba, sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.
Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
Duk, ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata;
babu wani lahani a cikinki.
Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.
Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.
Miji da mace ya halicce su.
Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
"Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo,
ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.
Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,
amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada."
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana.
"Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?