Publicidade

Bom dia

Por Bíblia Online

Cada manhã é presente de Deus. As misericórdias do Senhor se renovam cada dia. A Bíblia convida a começar o dia com louvor, oração e gratidão ao Criador.

Manhã com Deus

De manhã te apresentarei a minha oração. Pela manhã ouvirás a minha voz — eu te busco ao despertar.

Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;

da safe na gabatar da bukatuna a gabanka

in kuma jira da sa zuciya.

Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji;

da safe addu’ata kan zo gabanka.

Ka farka, raina!

Ku farka, garaya da molo!

Zan sa safe farka.

Amma zan rera game da ƙarfinka,

da safe zan rera game da ƙaunarka;

gama kai ne mafakata,

kagarata a lokacin wahala.

Amma zan rera game da ƙarfinka,

da safe zan rera game da ƙaunarka;

gama kai ne mafakata,

kagarata a lokacin wahala.

Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;

kai, ya Allah, kai ne kagarata,

Allah mai ƙaunata.

Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,

gama na sa zuciyata a gare ka.

Ka nuna mini hanyar da zan bi,

gama a gare ka na miƙa raina.

Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka;

sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.

Misericórdias renovadas

As misericórdias do Senhor se renovam cada manhã. Este é o dia que o Senhor fez — alegremo-nos e nos regozijemos nele.

Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

Sababbi ne kowace safiya;

amincinka kuwa mai girma ne.

Na ce wa kaina, "Ubangiji shi ne nawa;

saboda haka zan jira shi."

Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

Sababbi ne kowace safiya;

amincinka kuwa mai girma ne.

Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;

bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.

Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;

ku yabi sunansa mai tsarki.

Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

amma alherinsa har matuƙa ne;

mai yiwuwa a yi kuka da dare

amma farin ciki kan zo da safe.

Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

amma alherinsa har matuƙa ne;

mai yiwuwa a yi kuka da dare

amma farin ciki kan zo da safe.

Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka;

inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe

kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.

Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa,

don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.

Louvor matinal

Saciai-nos de manhã com a tua benignidade. Todo dia te louvarei e celebrarei o teu nome para sempre.

Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;

zan yabi sunanka har abada abadin.

Kowace rana zan yabe ka

in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.

Yana da kyau a yabi Ubangiji

a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

don a yi shelar ƙaunarka da safe

amincinka kuma da dare,

Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;

ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.

Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;

ku yi shelar cetonsa kowace rana.

Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,

manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka!

Ina tunani a kanta dukan yini.

Da rana Ubangiji yakan nuna ƙaunarsa,

da dare waƙarsa tana tare da ni,

addu’a ga Allah na raina.

Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai;

muna marmarinka.

Ka zama ƙarfinmu kowace safiya,

cetonmu a lokacin damuwa.

Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni,

don in san maganar da za ƙarfafa gajiyayye.

Ya farkar da ni da safe,

ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.

Graça para o novo dia

O Senhor te abençoe e te guarde. Cada novo dia é oportunidade de viver sob a graça do Deus que nos ama.

" ‘ "Ubangiji albarkace ku,

kuma kiyaye ku;

Ubangiji sa fuskarsa ta haskaka a kanku,

kuma yi muku alheri;

Ubangiji dube ku da idon rahama,

kuma ba ku salama." 

Ka shuka irinka da safe,

da yamma kuma kada ka janye hannunka,

gama ba ka san wanda zai yi albarka ba,

ko wannan ko wancan,

ko kuma duka biyunsu su yi albarka.

Takan farka tun da sauran duhu;

ta tanada wa iyalinta abinci

ta kuma shirya wa yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;

ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.

Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. Allah ya kira hasken "yini," ya kuma kira duhun "dare." Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.

Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku.

Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-