Pular para o conteúdo
Publicidade

Compaixão

Por Bíblia Online

A compaixão é o coração de Deus em ação. Ele é compassivo e misericordioso, tardio em irar-se e grande em amor. Somos chamados a refletir essa compaixão no mundo.

Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ya’yansa,

haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,

mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.

Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,

leɓunana za su ɗaukaka ka.

Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

Sababbi ne kowace safiya;

amincinka kuwa mai girma ne.

"Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta

ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?

Mai yiwuwa ta manta,

amma ba zan taɓa manta da ke ba!

Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;

katangarki kullum suna a gabana.

Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;

ya tashi don nuna muku jinƙai.

Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.

Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!

Wane ne Allah kamar ka,

wanda yake yafe zunubi kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?

Ba ka zama mai fushi har abada

amma kana marmari ka nuna jinƙai.

"Zan ƙarfafa gidan Yahuda

in kuma ceci gidan Yusuf.

Zan maido da su

domin ina jin tausayinsu.

Za su zama kamar

ban taɓa ƙinsu ba,

gama ni ne Ubangiji Allahnsu

zan kuma amsa musu.

"Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna. Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.

Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa.

Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

Shan wahala saboda yin ayyuka alheri

A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.

In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?

Allah na dukan ta’aziyya

Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.

Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba.

Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.

Gaisuwa ta ƙarshe

A ƙarshe yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.

Seja o primeiro