Confiabilidade
A confiabilidade de Deus é absoluta. Ele é fiel em todas as suas promessas, constante em seu amor e seguro em seu caráter. Podemos confiar nele completamente.
Deus é fiel
O Senhor é fiel em todas as suas palavras e bondoso em todos os seus atos. Grande é a sua fidelidade!
Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,
ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;
ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,
kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.
Amma daga madawwami zuwa madawwami
ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,
adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,
tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa
suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.
Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai
kuma ba zai yashe amintattunsa ba.
Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya,
’ya’yan mugaye za su hallaka.
Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.
Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa.
Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai."
Caráter de Deus
Toda boa dádiva vem do alto. O Senhor é bom e sua misericórdia dura para sempre. Nele podemos descansar.
Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji,
cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.
gama yana shayar da masu ƙishirwa
yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
Amma zan rera game da ƙarfinka,
da safe zan rera game da ƙaunarka;
gama kai ne mafakata,
kagarata a lokacin wahala.
Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
Integridade e confiança
Eu sou o Alfa e o Ômega — Deus é o mesmo ontem, hoje e sempre. Fiel em o que realizou e realizará por cada filho.
"Ni ne Alfa da kuma Omega," in ji Ubangiji Allah, "wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki."
Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada;
kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.
Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,
gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,
abubuwan da aka shirya tun da.
Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa;
gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.
Gulma yakan lalace yarda,
amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.
Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su,
amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.
"Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.