Consequências dos nossos atos
Toda ação tem consequências. A Bíblia ensina que colhemos o que semeamos — para o bem e para o mal. Deus pesará cada palavra e ato no dia do juízo.
Colher o que semear
Cada um prestará contas de si mesmo a Deus. O Senhor julgará as obras e os segredos dos homens com justiça perfeita.
Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.
Allah, "Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi." Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai, amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai. Gama Allah ba ya nuna bambanci.
Kyautar Allah kuwa ba kamar sakamakon da ya bi zunubin mutum gudan nan ba ne, Hukuncin ya bi zunubin mutum gudan nan, ya kuma kawo hallaka, amma kyautar ta bi laifofin masu yawa ta kuma sa Allah ya gan mu a matsayin marasa laifi. Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.
Ɗora wa waɗansu laifi
"Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.
Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.
Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke. Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.
Responsabilidade pessoal
Quem é sábio prevê o perigo e se esconde. A Palavra examina os pensamentos e intenções do coração.
Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka,
amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala.
In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada;
in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala."
Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani
daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
" ‘Mutum zai yi zunubi in bai yi magana ba sa’ad da ya ji ana shelar neman shaida game da wani abin da ya gani ko kuwa ya ji, alhakin zai zauna a wuyansa.
"In mutum ya yi zunubi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake bai sani ba, shi mai laifi ne. Za a kuwa nemi hakki daga gare shi.
" ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.
Consequências inevitáveis
A terra deu seu fruto conforme as obras dos que nela habitam. Ninguém escapa do juízo — Deus pesa cada ação.
Duniya za tă zama kufai saboda mazaunanta,
saboda ayyukansu.
Za ku sha hukuncin lalacinku ku kuma ɗauki hakkin zunuban bautar gumaka. Sa’an nan za ku san cewa Ni ne Ubangiji Mai Iko Duka."
Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.
Don me mugun mutum zai ƙi Allah?
Don me yakan ce wa kansa,
"Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba"?
Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki;
kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu.
Marar taimako kan danƙa kansa gare ka;
kai ne mai taimakon marayu