Consolador
O Espírito Santo é o Consolador prometido por Jesus. Ele consola os aflitos, fortalece os fracos e nos assegura que nunca estaremos sós.
O Consolador prometido
Jesus prometeu: Eu rogarei ao Pai e Ele vos dará outro Consolador para que fique convosco para sempre.
Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,
Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.
Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.
Aikin Ruhu Mai Tsarki
"Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni.
Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku.
Consolo divino
Bendito seja o Deus de toda consolação. Ele nos consola em toda tribulação e enxuga toda lágrima de nossos olhos.
Allah na dukan ta’aziyya
Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.
Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba.
Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu,
Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,
ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji,
ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.
‘Ba za su sāke jin yunwa ba;
ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba.
Rana ba za tă buga su ba,’
ko kuma kowane irin zafin ƙuna.
Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu;
‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’
‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ "
"Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku.
Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa,
’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,
Masu albarka ne waɗanda suke makoki,
gama za a yi musu ta’aziyya.