Publicidade

Consolo

Por Bíblia Online

O consolo de Deus é bálsamo para a alma ferida. Ele nos conforta em todas as tribulações para que possamos consolar outros com o mesmo consolo divino.

Deus consola

Ainda que eu ande pelo vale da sombra da morte, não temerei mal algum. O Senhor consola, guia e está sempre presente.

Ko da na yi tafiya

ta kwari na inuwar mutuwa,

ba zan ji tsoron mugu ba,

gama kana tare da ni;

bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

za su yi mini ta’aziyya.

Ta Dawuda.

Ubangiji ne haskena da cetona,

wa zan ji tsoro?

Ubangiji ne mafakar raina,

wane ne zan ji tsoro?

Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce

alkawarinka yana kiyaye raina.

Bari ƙaunarka marar ƙarewa yi mini ta’aziyya,

bisa ga alkawarinka ga bawanka.

Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,

ga kuma wanda yake neman shi;

Confiança na aflição

Eu sei que o meu Redentor vive. Deus é força e escudo — mesmo na tribulação, Ele nos sustenta e consola.

Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai,

kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.

Kuma bayan an hallaka fatata,

duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.

Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;

zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.

Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;

ya zama mai cetona."

Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai."

Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."

Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

"Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum zai iya yi mini?"

Masu albarka ne waɗanda suke makoki,

gama za a yi musu ta’aziyya.

Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,

ina sauraron Allah Mai Cetona;

Allahna kuwa zai ji ni.

Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.

Seja o primeiro
Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-29_22-07-56-