Publicidade

Conversão

Por Bíblia Online

A conversão é o ato de se voltar para Deus — arrependendo-se do pecado e abraçando a graça. É o início de uma vida nova, transformada pelo amor de Cristo.

Arrependei-vos

Arrependei-vos e convertei-vos para que os vossos pecados sejam apagados. A conversão começa com a mudança de mente e coração.

Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,

Bitrus ya amsa, "Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.

A Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba.

Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, "Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa."

Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.

Yana cewa, "Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!"

O amor de Deus converte

Céu se alegra por um pecador que se arrepende. Deus não deseja a morte do ímpio, mas que se converta e viva.

Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.

Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba."

Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba."

Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!

"Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.

Mutumin da ya yi zunubi zai mutu

Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, "Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa,

" Ubanni sun ci ya’yan inabi masu tsami,

haƙoran ya’ya kuwa sun mutu?

"Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba. Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.

"A ce akwai mai adalci

wanda yake aikata abin da yake daidai da kuma gaskiya;

ba ya cin abinci a duwatsun tsafi

ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.

Ba ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa

ko ya kwana da mace lokacin al’adarta ba.

Ba ya cin zalin wani,

amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa.

Ba ya yi fashi

amma yakan ba wa mayunwata abinci

ya kuma tanada wa marasa tufafi riga.

Ba ya ba da bashi da ruwa

ko ya karɓa ƙarin riba.

Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta

yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.

Yana bin ƙa’idodina

yana kuma kiyaye dokokina da aminci.

Wannan mutumin adali ne;

tabbatacce zai rayu,

in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

"A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba).

"Yakan ci abinci a duwatsun tsafi.

Yakan ƙazantar da matar maƙwabci.

Yakan ci zalin matalauta da mabukata.

Yakan yi fashi.

Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa.

Ya dogara ga gumaka.

Yana aikata ayyukan banƙyama.

Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa.

Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.

"Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato,

"Bai ci abinci a duwatsun tsafi ba

ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.

Bai ƙazantar da matar maƙwabcinsa ba.

Bai ci zalin wani

ko ya karɓi jingina ba.

Ba ya fashi

amma yakan ba da abincinsa ga mayunwata

ya tanada tufafi wa marasa tufafi.

Yakan janye hannunsa daga zunubi

ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa.

Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina.

Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu. Amma mahaifinsa zai mutu saboda zunubinsa, domin ya yi ƙwace, ya yi wa ɗan’uwansa fashi ya kuma yi abin da ba daidai ba a cikin mutanensa.

"Duk da haka kukan yi tambaya, Me ya sa ɗan ba zai sami rabo a laifin mahaifinsa ba?Da yake ɗan ya yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina, tabbatacce zai rayu. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za koma kansa.

"Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu. Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?

"Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.

"Duk da haka kun ce, Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce? In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu. Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa. Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba?

"Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba. Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila? Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!

Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani hallaka, sai dai kowa kai ga tuba.

Transformação

Voltai-vos para mim e sereis salvos! Rasgai o coração e não as vestes. A verdadeira conversão transforma o interior.

Bari mugu ya bar irin halinsa

mugu kuma ya sāke irin tunaninsa.

Bari juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa,

ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.

Na shafe laifofinka kamar girgije,

zunubanka kamar hazon safe.

Ka komo wurina,

gama na kuɓutar da kai."

Ku kyakkece zuciyarku

"Ko yanzu", in ji Ubangiji,

"Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku,

da azumi da kuka da makoki."

Ku kyakkece zuciyarku

ba rigunanku ba.

Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,

gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma

mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,

yakan kuma janye daga aika da bala’i.

in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

Hezekiya ya yi Bikin Ƙetarewa

Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu. Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba. Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.

Bisa ga umarnin sarki, sai yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa,

"Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya. Kada ku zama kamar iyayenku da yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani. Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi juye daga gare ku. In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama yan’uwanku da ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi."

Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a. Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima. Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.

Taron mutane mai girma ya haɗu a Urushalima don Bikin Burodi Marar Yisti a wata na biyu. Suka kawar da bagadai a Urushalima suka fid da bagadan turare suka zubar da su a Kwarin Kidron.

Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji. Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su. Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba. Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, "Bari Ubangiji, wanda yake nagari, gafarta wa kowa wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki." Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane.

Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.

Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu.

Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma. Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu. Taron gaba ɗaya na Yahuda suka yi farin ciki, tare da firistoci da kuma Lawiyawa da dukan waɗanda suka taru daga Isra’ila, har ma da baƙi waɗanda suka zo daga Isra’ila da waɗanda suke zama a Yahuda. Aka yi farin ciki mai girma a Urushalima, gama tun zamanin Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila, ba a taɓa yin wani abu kamar haka a Urushalima ba. Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki.

Kira don komawa ga Ubangiji

A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

"Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku. Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ku komo gare ni,in ji Ubangiji Maɗaukaki, ni kuma zan komo gare ku,in ji Ubangiji Maɗaukaki. Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji. Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne? Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku?

"Sa’an nan suka tuba suka ce, Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ "

Mutumin a cikin itatuwan ci-zaƙi

7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.

Sai na yi tambaya na ce, "Mene ne waɗannan ranka daɗe?"

Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, "Zan nuna maka mene ne su."

Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, "Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya."

Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, "Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya."

Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, "Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?" Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.

Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, "Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona, amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.

"Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,in ji Ubangiji Maɗaukaki.

"Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, kuma zaɓi Urushalima.’ "

Ƙahoni huɗu da maƙera huɗu

Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu! Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, "Mene ne waɗannan?"

Ya amsa mini ya ce, "Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima."

Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu. Na yi tambaya na ce, "Mene ne waɗannan suke zuwa yi?"

Ya amsa ya ce, "Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta."

Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.

Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.

Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci.

Yin alheri ga kowa

Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.

Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za iya cetonku.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-