Publicidade

Coragem

Por Bíblia Online

A coragem cristã não é ausência de medo — é confiança em Deus maior que todo temor. Sê forte e corajoso! é o chamado repetido do Senhor aos seus filhos.

Sê forte e corajoso

O Senhor é a minha luz e a minha salvação — de quem terei medo? Com coragem enfrentamos o mundo, porque Deus está conosco.

Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."

Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."

Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba."

Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba."

Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai."

Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, "Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji.

Coragem em Cristo

Não vos deu Deus espírito de covardia. Sede fortes na fé! O perfeito amor lança fora todo medo.

Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.

Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.

Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne.

Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, "Abba, Uba."

Não temas

Não temas, porque Eu sou contigo. Quando tiver medo, em ti confiarei. Deus é nosso escudo e fortaleza.

Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

Gama ni ne Ubangiji Allahnka,

wanda ya riƙe ka da hannun damana

ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;

zan taimake ka.

Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;

zan kawo yaranku daga gabas

in kuma tattara ku daga yamma.

"Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba.

Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba.

Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki

ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba.

Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

Ga Allah wanda maganarsa nake yabo

ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

Ubangiji ne haskena da cetona,

wa zan ji tsoro?

Ubangiji ne mafakar raina,

wane ne zan ji tsoro?

Ka dogara ga Ubangiji,

ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya

ka kuma dogara ga Ubangiji.

Ka dogara ga Ubangiji,

ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya

ka kuma dogara ga Ubangiji.

Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,

dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.

Ko da na yi tafiya

ta kwari na inuwar mutuwa,

ba zan ji tsoron mugu ba,

gama kana tare da ni;

bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

za su yi mini ta’aziyya.

Conforto e encorajamento

O Deus de toda consolação nos consola em todas as tribulações. Coragem não falta a quem descansa em Deus.

Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.

Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.

Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

"Ba zan taɓa bar ka ba;

ba zan taɓa yashe ka ba."

Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

"Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum zai iya yi mini?"

Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. "Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita."

Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.

Nan da nan ya yi magana da su ya ce, "Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro."

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-22_10-02-25-