Dar
Dar é princípio do Reino de Deus. Jesus deu tudo — até a própria vida. A Bíblia nos ensina que é mais bem-aventurado dar do que receber, e que Deus ama ao que dá com alegria.
Dar com alegria
Deus ama ao que dá com alegria. Dai e dar-se-vos-á. O generoso prospera e quem abençoa será abençoado.
Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.
Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.
To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa.
Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku."
Princípios de generosidade
Honra ao Senhor com as tuas primícias. Não negues o bem a quem o merece. A alma generosa prosperará.
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,
ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace,
sa’ad da kana iya yin haka.
Mutum mai kyauta zai azurta;
shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.
Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa
yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
Dukan yini yana marmari ya sami ƙari,
amma mai adalci yakan bayar hannu sake.
Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;
a tsare hakkin talakawa da masu bukata."
Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
O ensino de Jesus
Quando deres esmola, não toque a trombeta. A generosidade do coração importa mais que a grandeza do donativo.
"Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.
Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi, don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
Yesu ya amsa ya ce, "In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni."
Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka.
Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji
zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya,
amma masu adalci suna bayar hannu sake;
"Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.
Nehemiya ya ce, "Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku."
In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.