Publicidade

Dependência

Por Bíblia Online

A dependência de Deus é o caminho da verdadeira liberdade. Sem Cristo, nada podemos fazer. Mas em Deus encontramos sustento, direção e força para todo desafio.

Sem Ele nada podemos

Sem mim nada podeis fazer. O cristão que se desconecta da videira seca — mas o que permanece dá muito fruto.

"Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.

Ka kiyaye ni, ya Allah,

gama a cikinka nake samun mafaka.

Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,

masu gininta suna wahala a banza ne.

In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,

masu tsaro suna yin tsaro a banza.

Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar,

ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba;

hannun damanka ne, ƙarfin hannunka,

da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.

Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum."

Depender do Senhor

Confia no Senhor de todo o coração e não te estribes no teu próprio entendimento. Em todos os caminhos o reconhece.

Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

kada kuma ka dangana ga ganewarka;

cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu,

amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.

Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,

amma manufar Ubangiji ce takan cika.

Albarkar Ubangiji kan kawo wadata,

ba ya kuma ƙara wahala a kai.

Jikina da zuciyata za su iya raunana,

amma Allah ne ƙarfin zuciyata

da kuma rabona har abada.

Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki;

ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu,

za mu kuwa cetu.

Na da idanuna zuwa wajen tuddai,

ta ina ne taimakona zai zo?

Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

wanda ya kafa sama da ƙasa.

Ba zai bari ƙafarka yi santsi ba,

shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

Sa’ad da na ce, "Ƙafata na santsi,"

ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji,

ya kuwa amsa ta wurin yantar da ni.

Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,

yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

Contentamento e confiança

Aprendi a viver contente em toda situação. A dependência de Deus nos livra da ansiedade e nos firma na paz.

Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali.

Gama ni ne Ubangiji Allahnka,

wanda ya riƙe ka da hannun damana

ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;

zan taimake ka.

Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji

kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.

Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.

Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne.

Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

"Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-