Pular para o conteúdo
Publicidade

Despedida

Por Bíblia Online

As despedidas na Bíblia são momentos sagrados de bênção, oração e confiança em Deus. Mesmo na separação, os filhos de Deus se despedem com fé, carinho e esperança de reencontro.

Despedidas bíblicas

Paulo se despediu dos anciãos de Éfeso com oração e lágrimas. As despedidas entre irmãos são marcadas por afeto e fé.

Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a. Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba. Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.

Bulus ya ratsa Makidoniya da Giris

Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya.

Bayan suka yi yan kwanaki a can, sai yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.

Marmarin Bulus na ganin Tessalonikawa

Amma, yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku.

Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.

Amizades profundas

Davi e Jônatas se despediram com lágrimas e pacto de amizade. Rute se apegou a Noemi com lealdade inabalável.

Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsu, ya rusuna har sau uku. Sa’an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, Dawuda kuwa ya yi kuka sosai.

Yonatan ya ce wa Dawuda, "Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ " Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari.

Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsu, ya rusuna har sau uku. Sa’an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, Dawuda kuwa ya yi kuka sosai.

Sai Na’omi ta ce wa surukanta biyu, "Ku koma, kowannenku, zuwa gidan mahaifiyarta. Bari Ubangiji nuna muku alheri yadda kuka nuna wa matattun nan da kuma gare ni. Bari Ubangiji sa kowannenku ta sami hutu a gidan wani miji."

Sa’an nan ta sumbace su suka kuma yi kuka da ƙarfi suka ce mata, "Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki."

Amma Na’omi ta ce, "Ku koma gida, ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ya’ya maza da za su zama mazanku ne? Ku koma gida ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ya’ya maza, za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!"

A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata.

A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata.

Sa’an nan Musa ya sallame surukinsa Yetro, ya kuwa koma ƙasarsa.

Bênçãos de despedida

O Senhor te abençoe e te guarde. O Senhor faça resplandecer o seu rosto sobre ti e te dê a paz.

" ‘ "Ubangiji albarkace ku,

kuma kiyaye ku;

Ubangiji sa fuskarsa ta haskaka a kanku,

kuma yi muku alheri;

Ubangiji dube ku da idon rahama,

kuma ba ku salama." 

Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,

zai tsare ranka;

Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka

yanzu da har abada kuma.

Alheri kasance da ku duka.

Gaisuwa ta ƙarshe

A ƙarshe yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.

Gaisuwa ta ƙarshe

A ƙarshe yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.

Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.

Dukan tsarkaka suna gaishe ku.

Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.

Kayan yaƙi na Allah

A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji ba ku ƙarfi.

Sai Yoshuwa ya sa musu albarka, ya sallame su, suka kuwa tafi gidajensu.

Har wa yau, wani ya ce, "Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna."

Yesu ya amsa ya ce, "Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba."

Sai Elisha ya bar shanun, ya ruga ya bi Iliya. Ya ce, "Bari in sumbace mahaifina da mahaifiyata, in yi musu bankwana, sa’an nan in zo in bi ka."

Iliya ya ce, "Koma! Me na yi maka?"

Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa.

Seja o primeiro