O Deus do impossível
Deus é o Deus do impossível. Para Ele não há nada difícil demais. O que parece impossível aos olhos humanos é perfeitamente possível para o Criador do universo.
Nada é impossível
Para Deus nada é impossível. Ele faz infinitamente mais do que podemos pedir ou imaginar — esse é o nosso Deus.
Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne."
Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah."
Yesu ya amsa ya ce, "Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah."
Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, "Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?"
Mala’ikan ya amsa ya ce, "Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. Gama ba abin da zai gagari Allah."
Maryamu ta amsa ta ce, "To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa." Sai mala’ikan ya tafi abinsa.
Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, "Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’ Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa."
"Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa;
ba wanda zai iya ɓata shirinka.
"A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.
Fé no impossível
Se tiverdes fé como um grão de mostarda... Os impossíveis de Deus são convites ao exercício da fé audaciosa.
Ya amsa ya ce, "Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku."
Yesu ya ce, " ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata."
Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, "Mai yiwuwa ya zama da mamaki ga raguwar wannan mutanen da suke nan a lokacin, amma zai zama abin mamaki gare ni ne?" In ji Ubangiji Maɗaukaki.
Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;
ganewarsa ba shi da iyaka.
An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.