Deus é amor
Deus é amor — esta é a declaração mais profunda da Bíblia sobre a natureza divina. Tudo que Deus faz nasce do amor. Quem permanece no amor permanece em Deus.
A natureza de Deus
Deus é amor. Quem permanece no amor, permanece em Deus e Deus nele. Ele nos amou primeiro com amor eterno.
Ƙaunar Allah da kuma tamu
Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne.
Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.
Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.
Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.
Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
O amor de Deus revelado
Deus prova o seu amor em que Cristo morreu por nós quando ainda éramos pecadores. Seu amor é compassivo e eterno.
Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.
Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.
Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,
mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.
Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa!
Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.
Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,
leɓunana za su ɗaukaka ka.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi.
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
Wane ne Allah kamar ka,
wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?
Ba ka zama mai fushi har abada
amma kana marmari ka nuna jinƙai.
Gaisuwa ta ƙarshe
A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.