Deus nunca falha
Deus nunca falha. Nenhuma de suas promessas vem ao chão. O que Ele prometeu, Ele cumprirá. A fidelidade de Deus é o fundamento inabalável da nossa fé.
Promessas cumpridas
Nenhuma boa palavra falhou de todas as promessas que Deus fez. Ele é fiel e verdadeiro em tudo o que diz.
"Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.
Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alherin da ya yi wa mutanen Isra’ila.
"Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa.
Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,
shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.
Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?
Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada,
manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
Fidelidade eterna
A Palavra do Senhor permanece para sempre. A tua palavra é muito pura e o teu servo a ama profundamente.
Ku daga idanunku zuwa sammai
ku dubi duniya a ƙasa;
sammai za su ɓace kamar hayaƙi,
duniya za tă shuɗe kamar riga
mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje.
Amma cetona zai dawwama har abada,
adalcina ba zai taɓa kāsa ba.
An gwada alkawuranka sarai,
bawanka kuwa yana ƙaunarsu.
Mulkinka madawwamin mulki ne,
sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai.
Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa
mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi
yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.
Ubangiji da yake cikinki mai adalci ne;
ba ya yin abin da ba daidai ba.
Kowace safiya yakan bayyana dokokinsa a fili,
kowace sabuwar rana kuma ba ya kāsawa,
duk da haka marasa adalci ba sa jin kunya.
Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci;
tana zancen ƙarshe
kuma ba za tă zama ƙarya ba.
Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta;
lalle za tă zo, ba za tă makara ba.
Segurança em Deus
Todas as promessas de Deus são sim e amém em Cristo. Fiel é Aquele que prometeu — Ele jamais nos decepcionará.
Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar "Amin", domin a ɗaukaka Allah. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu, ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.
Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.
Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.