Publicidade

Deus

Por Bíblia Online

Deus é a realidade suprema do universo — o criador, sustentador e redentor de tudo o que existe. Conhecê-lo é a essência da vida eterna e o maior privilégio da existência humana.

Quem é Deus

Não há santo como o Senhor. Tu és grande e fazes maravilhas — só tu és Deus. Sua majestade transcende toda compreensão.

"Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji

babu wani, in ban da kai;

babu wani dutse kamar Allahnmu.

"Kai mai girma ne, ya Ubangiji Mai Iko Duka! Babu wani kamar ka, babu kuma wani Allah sai kai; kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.

Yabo ga Ubangiji

Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,

gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,

abubuwan da aka shirya tun da.

"Gama tunanina ba tunaninku ba ne,

yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,"

in ji Ubangiji.

Deus é amor

Deus é amor. Quem permanece no amor permanece em Deus e Deus nele. Nós amamos porque Ele nos amou primeiro.

Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.

Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.

Duk wanda ya ce, "Ina ƙaunar Allah," amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.

Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

Ubangiji Allahnki yana tare da ke,

mai iko ne don ceto.

Zai yi matuƙar farin ciki da ke,

zai rufe ki da ƙaunarsa,

zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa."

Buscar a Deus

Buscareis o Senhor e o encontrareis quando o buscardes de todo o coração. Provai e vede que o Senhor é bom.

Amma daga can in kuka nemi Ubangiji Allahnku, da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, za ku same shi.

Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;

mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

Na ce wa Ubangiji, "Kai ne shugabana;

in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau."

Wa nake da shi a sama in ba kai ba?

Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata,

saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.

Gama duk wanda ya same ni ya sami rai

zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

Viver com Deus

Sê forte e corajoso, porque o Senhor teu Deus é contigo. Em Deus encontramos a razão de existir.

Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."

Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

Gargaɗi

Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!

Ɗaukakar Sihiyona

"Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo,

ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.

Gama ni ne Ubangiji Allahnka,

wanda ya riƙe ka da hannun damana

ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;

zan taimake ka.

Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.

Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.

Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-