Dia das crianças
As crianças são preciosas aos olhos de Deus. Jesus as acolheu, abençoou e ensinou que delas é o Reino dos Céus — modelos de fé, pureza e humildade.
Jesus e as crianças
Deixai vir a mim as crianças. Jesus abraçou, abençoou e honrou as crianças como modelo de fé para os adultos.
Yesu ya ce, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne."
Mafi girma a mulkin sama
A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, "Wane ne mafi girma a mulkin sama?"
Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. Sai ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama.
Misalin ɓatacciyar tunkiya
"Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.
Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, "Hosanna ga Ɗan Dawuda," sai fushi ya kama su.
Suka tambaye shi suka ce, "Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?"
Yesu ya amsa ya ce, "I, ba ku taɓa karanta ba cewa,
" ‘Daga leɓunan yara da jarirai
kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?"
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba." Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.
Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu, "Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa."
Instruir e proteger
Instrui a criança no caminho de Deus. Elas são herança do Senhor — presentes sagrados que devemos educar com amor.
Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza,
da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.
’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,
yara lada ne daga gare shi.
’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.
Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
’Ya’ya da iyaye
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
" ‘ "Ubangiji yă albarkace ku,
yă kuma kiyaye ku;
Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku,
yă kuma yi muku alheri;
Ubangiji yă dube ku da idon rahama,
yă kuma ba ku salama." ’