Pular para o conteúdo
Publicidade

Dia dos avós

Por Bíblia Online

Os avós são tesouros vivos de sabedoria e fé. A Bíblia honra os mais velhos e celebra a transmissão de fé entre gerações — dos avós aos netos e destes aos que virão.

A bênção dos avós

A coroa dos velhos são os filhos dos filhos. A misericórdia de Deus é de geração em geração sobre os que o temem.

Jikoki rawanin tsofaffi ne,

kuma iyaye su ne abin taƙamar ya’yansu.

Amma daga madawwami zuwa madawwami

ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,

adalcinsa kuma tare da ya’yansu,

ni yaro ne amma yanzu na tsufa,

duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba

ko a ce ya’yansu suna roƙon burodi.

Tsara guda za yi maganar ayyukanka ga wata tsara;

za su yi magana game da manyan ayyukanka.

Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;

amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.

Força e fidelidade

Mesmo na velhice darão frutos. Os cabelos brancos são coroa de glória. Deus não abandona seus filhos na idade avançada.

Za su ci gaba da ba da ya’ya a tsufansu,

za su kasance ɗanye kuma kore shar,

suna shela cewa, "Ubangiji adali ne;

shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa."

Furfura rawani ne mai daraja;

akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.

Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura

ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.

Na yi ku zan kuma riƙe ku;

zan lura da ku

in kuma kuɓutar da ku.

Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

za su sabunta ƙarfinsu.

Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ya’yanku, da ya’yan ya’yanku.

Seja o primeiro