Pular para o conteúdo
Publicidade

Dia dos pais

Por Bíblia Online

O Dia dos Pais celebra o amor e o sacrifício paterno. A Bíblia honra os pais como provedores, protetores e guias espirituais que moldam as próximas gerações.

O pai que educa

Instrui a criança no caminho em que deve andar. O pai justo educa com amor, firmeza e o exemplo de uma vida íntegra.

Ka hori yaro a hanyar da ya kamata bi,

kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,

amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.

Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;

masu albarka ne ya’yan da za su biyo bayansa.

Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;

duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,

kuma ga ya’yansa zai zama mafaka.

Honra e alegria

Honra a teu pai e tua mãe. Os filhos são herança do Senhor, e a família que serve a Deus junta é inabalável.

Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

haka ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

Mai albarka ne mutumin

da korinsa sun cika da su.

Ba za a kunyata su ba

sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.

Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.

"Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

"Sai ɗan ya ce masa, Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.

"Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali.

Seja o primeiro