Publicidade

Dificuldades

Por Bíblia Online

As dificuldades são parte da vida, mas Deus é refúgio certo em todo tempo de angústia. A Bíblia promete que nenhuma adversidade pode separar os filhos de Deus do seu amor.

Deus é refúgio

Deus é nosso refúgio e fortaleza, socorro bem presente nas angústias. Nada poderá nos separar do amor de Cristo.

Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

kullum yana a shirye taimaka a lokacin wahala.

Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza

duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

ko da ruwansa suna ruri suna kumfa

duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

Zan ce game da Ubangiji, "Shi ne mafakata da kagarata,

Allahna, wanda nake dogara."

Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;

ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,

gama Allah ne mafakarmu. Sela

Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,

mafaka a lokutan wahala.

Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,

gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

Kana mulkin teku mai tumbatsa;

sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su.

Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye,

mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku,

Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.

Ya kwantar da hadiri suka yi tsit;

raƙuman ruwan teku suka yi shiru.

Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? Kamar yadda yake a rubuce cewa,

"Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;

an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka."

A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Provisão nas dificuldades

O Senhor provê mesmo nos tempos mais difíceis. Ele sustentou Elias, protegeu Israel e cuida dos seus com fidelidade eterna.

Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya.

Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi,

da kuma wuta don ta ba su haske da dare.

Suka roƙa, ya kuwa ba su makware

ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama.

Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo,

kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada.

ni yaro ne amma yanzu na tsufa,

duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba

ko a ce ya’yansu suna roƙon burodi.

Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji,

kuma gādonsu zai dawwama har abada.

A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba;

a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.

Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa,

rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa;

zan ba da Ruhuna ga ya’yanka,

albarkata kuma ga zuriyarka.

Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa,

wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana.

Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango

Za zama rumfa da inuwar da za tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama.

Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,

zan kasance tare da ku;

sa’ad da kuka bi ta koguna,

ba za su kwashe ku ba.

Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,

ba za ƙone ku ba;

harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.

Força nas provas

Em tudo somos atribulados, mas não esmagados. O Senhor é bom e é fortaleza no dia da angústia — Ele conhce os seus.

A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba.

Ubangiji nagari ne,

mafaka kuma a lokacin wahala.

Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,

Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,

duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.

Ya rufe fuskar wata,

ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,

ya zāna iyakar fuskar ruwa

a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.

Zai kāre ka daga ɓata suna,

kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo.

Ya amsa ya ce, "Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?" Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

Mutanen suka yi mamaki suka ce, "Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!"

In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? Don haka, kada ku damu, kuna cewa, Me za mu ci?Ko, Me za mu sha?Ko kuma, Me za mu sa?

Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260.

Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-