Pular para o conteúdo
Publicidade

Domínio próprio

Por Bíblia Online

O domínio próprio é fruto do Espírito e marca de maturidade espiritual. A Bíblia ensina que quem governa o próprio espírito é melhor do que quem conquista uma cidade.

Fruto do Espírito

O fruto do Espírito inclui domínio próprio. A graça de Deus nos ensina a viver de maneira sóbria e justa neste mundo.

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. Yana koya mana mu ce, "A’a" ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-shaawacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,

Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga yan’uwa; ga nuna alheri ga yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna.

Governar a si mesmo

Melhor é o que domina o seu espírito do que o que toma uma cidade. A cidade sem muros é o homem sem domínio próprio.

Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi,

ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

Kamar birni da katangarsa sun rushe

haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa.

Wawa yakan nuna fushinsa a fili,

amma mai hikima kan kanne fushinsa.

Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki,

amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.

Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada. Duk yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.

Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

Disciplina e vigilância

Sede sóbrios e vigilantes. O diabo anda em derredor como leão rugidor. A sobriedade nos protege e fortalece.

Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a.

Rayuwa saboda Allah

Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-shaawacen jiki, sai dai nufin Allah. Gama kun ɓata lokaci sosai a kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-shaawace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye shari’anta masu rai da matattu.

don kowannenku koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;

O senhorio de Cristo

Todo domínio pertence a Cristo. Ele é Senhor dos senhores e Rei dos reis — e nos capacita a viver em santidade.

Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa

ko’ina a mulkinsa.

Yabi Ubangiji, ya raina.

Mulkinka madawwamin mulki ne,

sarautarka kuma za dawwama cikin dukan zamanai.

Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa

mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.

"A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum suna nufin mutum. Kalmomin nan ɗan mutum an yi amfani da su a nan saboda a amfanin da aka yi da su a Sabon Alkawari a matsayi wakilin suna na Yesu, mai yiwuwa saboda dangane a kan wannan ayar. yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.

Ina murna in shaida muku game da alamu da al’ajabai waɗanda Allah Mafi Ɗaukaka ya yi ta wurina.

Alamunsa da girma suke,

ayyukansa da girma suke!

Mulkinsa mulki ne na har abada;

sarautarsa kuma za dawwama daga zamani zuwa zamani.

Gama a gare mu an haifa mana yaro,

a gare mu an ba da ɗa,

gwamnati za kasance a kafaɗarsa.

Za a ce da shi

Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki

Uban Madawwami, Sarkin Salama.

Game da girmar gwamnatinsa da salama

babu iyaka.

Zai gāji sarki Dawuda, yi mulki a matsayinsa,

zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,

tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.

Ubangiji Maɗaukaki ne

ya yi niyyar aikata wannan duka.Ubangiji

Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

da ya da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.

Amma mu yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

Gama mun san cewa da yake an da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa.

Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.

Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.

Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi. Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a da waɗanda suke nasa. Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. Gama dole yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.

"Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;

yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.

Seja o primeiro