Pular para o conteúdo
Publicidade

Esperança

Por Bíblia Online

A esperança cristã não é desejo vago — é certeza inabalável fundamentada nas promessas de Deus. Ela é âncora da alma, firme e segura, que penetra até o interior do véu.

Esperança viva

Bendito seja Deus que nos gerou de novo para uma esperança viva, mediante a ressurreição de Jesus Cristo.

Yabo ga Allah domin bege mai rai

Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,

Yabo ga Allah domin bege mai rai

Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,

Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,

Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,

Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.

Esperança que não decepciona

A esperança não decepciona, pois o amor de Deus é derramado em nossos corações pelo Espírito Santo.

Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

Salama da farin ciki

Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah.

Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege.

Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.

Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.

Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.

Bari Allah na bege cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

Bari Allah na bege cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

A fé é a certeza

A fé é a certeza do que se espera. Mantenhamos firme a confissão da esperança, pois fiel é o que prometeu.

Ta wurin bangaskiya

Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba.

Ta wurin bangaskiya

Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba.

Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.

Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.

Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku.

Ina kuma addu’a cewa zuciyarku waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa.

Su ne Allah ya so sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.

Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar

Esperança e confiança

Eu sei os planos que tenho para vocês — planos de paz e esperança. Deus é a fonte de toda esperança.

Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.

Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.

Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,

dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.

Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,

dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.

Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da kuma Allahna.

Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da kuma Allahna.

Kai ne mafakata da garkuwata;

na sa zuciyata a maganarka.

Kai ne mafakata da garkuwata;

na sa zuciyata a maganarka.

Raina ya tafke da marmari don cetonka,

amma na sa zuciyata a maganarka.

Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa,

wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.

A gare ka na dogara, ya Allahna.

Kada ka bari in sha kunya,

ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.

Ba wanda yake sa bege a gare ka

da zai taɓa shan kunya,

amma za su sha kunya

su da suke tayarwa babu dalili.

Esperança eterna

Somos salvos na esperança. Aquele que prometeu é fiel. A esperança está guardada nos céus para os que creem.

wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami.

Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.

wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.

Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.

Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.

Zuwan Ubangiji

Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.

Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan.

Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

Expressões de esperança

Vinde a mim todos os que estais cansados. A esperança adia a dor e floresce na presença do Senhor.

"Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.

Shekarar tagomashin Ubangiji

Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

domin Ubangiji ya shafe ni

domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.

Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,

don in yi shelar yanci don ɗaurarru

in kuma kunce yan kurkuku daga duhu

amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

za su sabunta ƙarfinsu.

Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

Na ce wa kaina, "Ubangiji shi ne nawa;

saboda haka zan jira shi."

Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,

ina sauraron Allah Mai Cetona;

Allahna kuwa zai ji ni.

Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya yi ciwo,

amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.

Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya yi ciwo,

amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.

Firmeza na esperança

Esperai no Senhor! O cavalo é vaidade para a segurança, mas o Senhor guarda os que nele esperam.

Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,

ko ma da muke sa begenmu a gare ka.

Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,

ko ma da muke sa begenmu a gare ka.

Muna jiran Ubangiji da bege;

shi ne taimakonmu da garkuwarmu.

Dogara a kan doki don ceto banza ne;

duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.

Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,

a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,

don cece su daga mutuwa

ya bar su da rai a lokacin yunwa.

Zan jira Ubangiji, raina zai jira,

kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;

dogarata kan zo daga gare shi ne.

Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci,

Ya Allah Mai Cetonmu,

begen dukan iyakar duniya

da kuma na tekuna masu nesa,

"Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema?

Begena yana a gare ka.

ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,

gama kai ne Allah Mai cetona,

kuma begena yana a kanka dukan yini.

Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;

da safe na gabatar da bukatuna a gabanka

in kuma jira da sa zuciya.

Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba,

ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.

Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,

zai tsare ranka;

Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka

yanzu da har abada kuma.

Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

Seja o primeiro