Esperar no Senhor
Esperar no Senhor é ato de fé e confiança. A Bíblia promete que os que esperam em Deus renovam as forças, recebem direção e experimentam a fidelidade divina no tempo certo.
Renovar as forças
Os que esperam no Senhor renovam as forças. Sobem como águias, correm e não se cansam, caminham e não se fatigam.
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;
ya tashi don yă nuna muku jinƙai.
Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.
Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!
Ka dogara ga Ubangiji,
ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya
ka kuma dogara ga Ubangiji.
Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa
zan ga alherin Ubangiji;
a ƙasar masu rai.
Ka dogara ga Ubangiji,
ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya
ka kuma dogara ga Ubangiji.
Ubangiji ne haskena da cetona,
wa zan ji tsoro?
Ubangiji ne mafakar raina,
wane ne zan ji tsoro?
Sa’ad da mugaye suka tasar mini
don su cinye ni,
sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,
sun yi tuntuɓe suka fāɗi.
Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni,
zuciyata ba za tă ji tsoro ba;
ko da yake ya ɓarke a kaina,
duk da haka zan ƙarfafa.
Abu guda na roƙi Ubangiji,
wannan shi ne na nema,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
dukan kwanakin raina,
in dubi kyan Ubangiji
in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
Gama a lokacin wahala,
zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa;
zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa
ya kuma sa ni can a bisa dutse.
Sa’an nan kaina zai ɗaukaka
a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni;
a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki;
zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.
Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji;
ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini.
Zuciyata kan faɗa game da kai, "Nemi fuskarsa!"
Fuskarka, Ubangiji, zan nema.
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni,
kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi;
kai ne ka kasance mai taimakona.
Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni,
Ya Allah Mai cetona.
Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni,
Ubangiji zai karɓe ni.
Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji;
ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya
saboda masu danne ni.
Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina,
gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina,
suna numfasa tashin hankali.
Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa
zan ga alherin Ubangiji;
a ƙasar masu rai.
Ka dogara ga Ubangiji,
ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya
ka kuma dogara ga Ubangiji.
Espera paciente
Esperei com paciência no Senhor e Ele se inclinou para mim. Confie nele e descanse — Ele agirá no tempo certo.
Na jira da haƙuri ga Ubangiji;
ya juya wurina ya kuma ji kukata.
Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,
daga laka da taɓo;
ya sa ƙafafuna a kan dutse
ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.
Ya sa sabuwar waƙa a bakina,
waƙar yabo ga Allahna.
Da yawa za su gani su tsorata
su kuma dogara ga Ubangiji.
Mai albarka ne mutumin
da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,
wanda ba ya kula da masu girman kai,
waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna,
abubuwan banmamakin da ka aikata.
Abubuwan da ka shirya mana.
Ba wanda zai iya faɗa maka su;
a ce zan yi magana in faɗe su,
za su wuce gaban misali a furta.
Hadaya da sadaka ba ka sha’awa,
amma kunnuwana ka huda;
hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.
Sa’an nan na ce, "Ga ni, na zo,
kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.
Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna;
dokar tana cikin zuciyata."
Na yi shelar adalcinka cikin babban taro;
ba na rufe leɓunana,
kamar yadda ka sani, ya Ubangiji.
Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata;
ina maganar amincinka da cetonka.
Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka
a gaban taron jama’arka mai girma ba.
Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;
bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni;
zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani.
Sun fi gashin kaina yawa,
har ma na fid da zuciya.
Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji;
Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.
Bari masu neman raina
su sha kunya su kuma rikice;
bari dukan waɗanda suke neman lalacewata
su koma baya da kunya.
Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
A cikinsa zukatanmu na farin ciki,
gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,
ko ma da muke sa begenmu a gare ka.
Zan jira Ubangiji, raina zai jira,
kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
Raina na jiran Ubangiji
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;
dogarata kan zo daga gare shi ne.
Ku sa zuciya ga Ubangiji
ku kuma kiyaye hanyarsa.
Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar,
sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.
Confiança e perseverança
Confie no Senhor de todo o coração. Sede pacientes na tribulação — o Senhor é fiel e cumprirá todas as suas promessas.
Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege.
Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki
Haƙuri cikin wahala
Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.
Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.
Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. Gama,
"Dukan mutane kamar ciyawa suke,
darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;
ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,
amma maganar Ubangiji tana nan har abada."
Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.
Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
Misalin budurwai goma
"A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.
"Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’
"Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’
"Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’
"Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.
"An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’
"Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’
"Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.