Pular para o conteúdo
Publicidade

Evangelização

Por Bíblia Online

A evangelização é a missão suprema da Igreja. Jesus mandou: ide por todo o mundo e pregai o evangelho a toda criatura. O evangelho é poder de Deus para a salvação de todo aquele que crê.

A Grande Comissão

Ide, fazei discípulos de todas as nações. Jesus confiou a seus seguidores a missão de levar a boa notícia ao mundo inteiro.

Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin da Gal 3.27 sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani."

Ya ce, musu, "Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.

Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya."

"Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.

Gishiri da kuma haske

"Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.

Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. Haka ma, bari haskenku haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, "Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa."

O poder do evangelho

O evangelho é poder de Deus para a salvação. A fé vem pelo ouvir, e o ouvir pela Palavra de Cristo.

Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai.

Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.

Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.

Tashin matattu na Kiristi

To, yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai. Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan.

Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.

Testemunhar e proclamar

Estai sempre preparados para responder com mansidão a todo aquele que pedir razão da vossa esperança.

Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,

Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna."

Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.

Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa,

" Na sa ka zama haske ga Al’ummai,

don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya."

Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

"Ruhun Ubangiji yana kaina,

domin ya shafe ni,

in yi wa matalauta wa’azin bishara.

Ya aiko ni in yi shelar yanci ga yan kurkuku,

in kuma buɗe idanun makafi,

in ba da yanci ga waɗanda aka danne.

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, sa’an nan kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da yan’uwa mata, da yan’uwa maza, da uwaye, da ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma sami rai madawwami.

Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.

Fazer conhecer

Dai graças ao Senhor, invocai o seu nome, fazei conhecidas as suas obras entre os povos.

Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

A wannan rana za ku ce,

"Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,

a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.

Su ne Allah ya so sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.

Abin da ya kamata a koyarwa wa ƙungiyoyi dabam-dabam

Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa.

Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.

Seja o primeiro