Família de Deus
A família de Deus transcende laços de sangue. Em Cristo, somos adotados como filhos, irmãos uns dos outros e membros de uma família eterna — a Igreja.
Adotados por Deus
Recebemos o espírito de adoção pelo qual clamamos: Abba, Pai! Se filhos, também herdeiros — herdeiros de Deus e co-herdeiros com Cristo.
Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, "Abba, Uba." Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne. In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.
Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, "Abba, Uba." Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan. Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu.
A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.
Addu’a saboda Afisawa
Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna.
Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.
A comunidade de fé
Não abandonem a congregação. Somos um corpo em Cristo, membros uns dos outros, chamados a amar e a servir.
Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.
Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.
haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne.
In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.
Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.
Quem é minha família?
Jesus disse: quem faz a vontade de Deus, esse é meu irmão e irmã. A família de Deus inclui todos os que creem.
Ya yi tambaya ya ce, "Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?"
Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, "Ga mahaifiyata da ’yan’uwana! Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata."
Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.
’Ya’yan Iblis
Yesu ya ce musu, "Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni.
Shawara game da gwauraye, dattawa da kuma bayi
Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka, tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.