Filho do homem
Filho do Homem é o título que Jesus mais usou para si mesmo. Ele conecta sua humanidade plena com a visão profética de Daniel sobre o Messias glorioso que receberá domínio eterno.
A profecia de Daniel
Daniel viu alguém como o Filho do Homem vindo com as nuvens do céu. Foi-lhe dado domínio, glória e reino eterno.
"A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum suna nufin mutum. Kalmomin nan ɗan mutum an yi amfani da su a nan saboda a amfanin da aka yi da su a Sabon Alkawari a matsayi wakilin suna na Yesu, mai yiwuwa saboda dangane a kan wannan ayar. yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.
A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani "kama da ɗan mutum,". saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa.
Girbin duniya
Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar "ɗan mutum". tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa.
Ya ce, "Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah."
Jesus, o Filho do Homem
O Filho do Homem veio buscar e salvar o que se havia perdido. Ele tem autoridade para perdoar pecados e julgar.
Ya amsa ya ce, "Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum.
Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.
Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, "Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane.
Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.
Tumaki da awaki
"Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.
gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, "Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi."
Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa."
Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai." Sai ya ce wa shanyayyen, "Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida."
Yesu ya ce, "Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa."
Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa.
Glória e autoridade
Quando o Filho do Homem for levantado, atrairá todos a si. Ele é plenamente humano e plenamente divino.
Saboda haka Yesu ya ce, "Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.
Sai ya ƙara da cewa, "Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum."
Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa,
"Mene ne mutum, da kake tuna da shi,
ɗan mutum da kake kula da shi?