Pular para o conteúdo
Publicidade

Filhos de Deus

Por Bíblia Online

Ser filho de Deus é o maior privilégio da existência humana. Pela fé em Cristo, recebemos o direito de ser chamados filhos de Deus — herdeiros de Deus e co-herdeiros com Cristo.

O direito de ser filho

A todos que creram no nome de Jesus, deu-lhes o poder de serem feitos filhos de Deus — nascidos não do sangue, mas de Deus.

Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ya’yan Allah ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada hallaka sai dai sami rai madawwami.

An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

Dukanku ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan.

Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ya’ya.

Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.

A identidade dos filhos

O Espírito testifica com nosso espírito que somos filhos de Deus. E se filhos, também herdeiros — herdeiros de Deus.

Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ya’yan Allah. Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, "Abba, Uba."

Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ya’yan Allah ne.

Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.

"Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, Ku ba mutanena ba ne,za a kira su ya’yan Allah mai rai.

Abinci mai tsabta da marar tsabta

Ku ya’yan Ubangiji Allahnku ne. Kada ku yi wa kanku zāne, ko ku yi wa kanku aski irin da akan bar sanƙo, saboda wanda ya mutu, gama ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Daga dukan mutane a fuskar duniya, Ubangiji ya zaɓe ku, ku zama abin mallakarsa.

Viver como filhos

Vede que grande amor o Pai nos concedeu: que fôssemos chamados filhos de Deus! E é isso que somos.

Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba san mu ba shi ne, don ba san shi ba.

Ta haka muka san waɗanda suke ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,

gama za a kira su ya’yan Allah.

Ya tambaye su, "Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?"

Siman Bitrus ya amsa ya ce, "Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai."

Yesu ya amsa ya ce, "Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.

Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ya’yan gida ba.

Seja o primeiro