Publicidade

Generosidade

Por Bíblia Online

A generosidade é marca do caráter de Deus e vocação do cristão. Deus ama ao que dá com alegria. Quem semeia generosamente, generosamente colherá.

Dar com alegria

Deus ama ao que dá com alegria. Cada um contribua segundo propôs no coração — não com tristeza ou por necessidade.

Ya kamata kowa bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.

Shukin yardar rai

Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. Ya kamata kowa bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. Allah kuwa yana da iko ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. Kamar yadda yake a rubuce cewa,

"Ya ba gajiyayyu hannu sake,

ayyukansa na alheri madawwama ne."

To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, riɓanya shi, kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za zama sanadin godiya ga Allah.

Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.

To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, riɓanya shi, kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa.

Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za zama sanadin godiya ga Allah.

Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.

Partilhar e abençoar

Quem dá aos pobres empresta ao Senhor. A generosidade abre portas de bênção sobre quem dá e sobre quem recebe.

Mutum mai kyauta zai azurta;

shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.

Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye;

wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.

Mutum mai kyauta zai azurta;

shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.

Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,

ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;

ta haka rumbunanka za su cika har su zuba,

randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.

Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace,

sa’ad da kana iya yin haka.

In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci,

shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.

Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.

O ensino de Jesus

Dai e dar-se-vos-á. A quem te pedir, dá. O que fizestes a um destes mais pequeninos, a mim o fizestes.

Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku."

Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku."

Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema mayar maka.

In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!"

Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.

"Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka ma san abin da hannun damarka yake yi, don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

"Sarkin zai amsa ya ce, Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.

Generosidade de Deus

Se Deus dá sabedoria generosamente a quem pede, quanto mais nos dará Ele forças e suprimento em toda necessidade?

In waninku ya rasa hikima, ya kamata roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

A ce wani ɗan’uwa ko yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, sai waninku ce masa, "Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura," amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.

Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji

kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.

Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,

shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-