Publicidade

Gentileza

Por Bíblia Online

A gentileza é fruto do Espírito e marca do cristão maduro. Palavras suaves, gestos de bondade e amor ao próximo — a Bíblia nos chama a tratar todos com graça e compaixão.

Seja gentil

A vossa gentileza seja conhecida de todos. A palavra branda desvia a ira, e a boa conduta atrai os que estão distantes.

Bari kowa kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi,

amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.

Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,

mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.

Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa.

Gentileza como fruto

O fruto do Espírito inclui bondade e amabilidade. Amem uns aos outros com afeição fraternal e tratem bem a todos.

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

Gargaɗin ƙarshe

Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar yan’uwa. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba.

Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba.

" Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

" Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.

"Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna. Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.

Gaskiya nake gaya muku, Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ "

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-