Publicidade

Gratidão a Deus

Por Bíblia Online

A gratidão a Deus é atitude que transforma a vida. Reconhecer que toda boa dádiva vem de Deus nos leva a louvar, servir e viver com alegria e propósito.

Tudo vem de Deus

Toda boa dádiva vem do alto. Agradecer a Deus é reconhecer que Ele é a fonte de toda bênção e sustento.

Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya,

Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.

Alherin Ubangiji ga Bulus

Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa.

Umarnai a kan sujada

Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’oi, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum

kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske.

ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.

Ku bar salamar Kiristi yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

Louvor e gratidão

Louvai ao Senhor e dai-lhe graças! Ele fez maravilhas e é digno de todo louvor e agradecimento.

Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa

zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.

"Ku miƙa hadayar godiya ga Allah,

ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,

Zan yabe sunan Allah cikin waƙa

in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.

Amma bari dukan masu nemanka

su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka;

bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce,

"Bari Allah sami ɗaukaka!"

Muna maka godiya, ya Allah,

muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa;

mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.

Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka,

za mu yabe ka har abada;

daga tsara zuwa tsara

za mu yi ta ba da labarin yabonka.

Ku shiga ƙofofinsa da godiya

filayen gidansa kuma da yabo;

ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

Ka mai da kukata ta zama rawa;

ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

don zuciyata za iya rera gare ka ba kuwa za yi shiru ba.

Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.

Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;

ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

ƙaunarsa madawwamiya ce.

Expressões de gratidão

Dar graças com oração e súplica. A gratidão se expressa em palavras, atos e atitudes que glorificam a Deus.

Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.

Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.

Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za zama sanadin godiya ga Allah.

Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.

ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

suna cewa,

"Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,

wanda yake a yanzu, shi ne kuma a ,

domin ka karɓi ikonka mai girma

ka kuma fara mulki.

Amma ni, da waƙar godiya,

zan miƙa tawa hadaya gare ka.

Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi.

Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji."

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-