Guardar o coração
Guardar o coração é o mandamento mais urgente de Provérbios. Sobre tudo o que se deve guardar, guarda o teu coração, porque dele procedem as fontes da vida.
Sobre tudo, guarda o coração
O coração é a nascente de tudo — pensamentos, desejos, decisões. Guardá-lo é proteger toda a vida espiritual e emocional.
Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,
gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
Faɗi 18
Ɗana, ka ba ni zuciyarka
bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,
Ƙarin ribar hikima
Ɗana, kada ka manta da koyarwata,
amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa
su kuma kawo maka wadata.
Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne."
Coração puro e renovado
Cria em mim um coração puro, ó Deus. Os puros de coração verão a Deus — e o Espírito renova nosso interior.
Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,
ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,
gama za su ga Allah.
Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata;
ka gwada ni ka kuma san damuwata.
Duba ko akwai wani laifi a cikina,
ka bishe ni a madawwamiyar hanya.
Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni,
ka bincike zuciyata da tunanina;
gama ƙaunarka kullum tana a gabana,
kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
Ko ka duba zuciyata,
ka kuma bincike ni da dare,
ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba;
na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.
Game da ayyukan mutane kuwa,
ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina
daga hanyoyin tashin hankali.
Sawuna sun kama hanyoyinka
ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.
Zuciyata tana nan daram, ya Allah,
zuciyata tana nan daram;
zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
Guardar com a Palavra
Não vos conformeis com este mundo. A Palavra de Deus guardada no coração nos protege do pecado e nos direciona.
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.
Na neme ka da dukan zuciyata;
kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.
Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata
don kada in yi maka zunubi.
Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku.
ya ce musu, "Ku riƙe dukan kalmomin da na furta muku a yau, don ku umarce ’ya’yanku su lura, su yi biyayya da dukan kalmomin wannan doka.
Vigilância e paz
A paz de Deus guarda nossos corações em Cristo Jesus. Chegai-vos a Deus, purificai os corações — e Ele estará convosco.
Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.
Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.
Umarnai don zaman tsarki
Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah.