Homem
A Bíblia fala sobre o homem como criação de Deus — feito à sua imagem e semelhança, mas também frágil, mortal e necessitado de redenção.
Criado à imagem de Deus
Deus criou o homem à sua imagem. Mas pelo pecado, o homem caiu e passou a depender da graça para ser restaurado.
Sa’an nan Allah ya ce, "Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa."
Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.
Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.
Miji da mace ya halicce su.
Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.
Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi.
Haka yake a rubuce cewa, "Adamu, mutumin farko ya zama mai rai"; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.
Fragilidade humana
O homem nascido de mulher é de poucos dias e cheio de inquietação. Deus conhece nossa fragilidade e cuida de nós.
"Mutum haihuwar mace
kwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala.
‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci,
ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?
"Mene ne mutum har da ka kula da shi haka,
har ka mai da hankali a kansa,
Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa,
"Mene ne mutum, da kake tuna da shi,
ɗan mutum da kake kula da shi?
Ubangiji ne yake bi da matakan mutum,
Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?
Renovação e chamado
Despojados do velho homem e revestidos do novo, somos chamados a buscar a justiça, a piedade e o amor.
sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.
Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu.
Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.
Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata.
Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji,
yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.
Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke,
amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.
A confiança errada
Maldito o homem que confia no homem. O homem de duplo ânimo é instável em todos os seus caminhos.
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
"La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,
wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi
wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.
Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji; shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.
Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka,